Watakila sai mun rufe makarantu kaf saboda satar ‘dalibai da ake yi inji NANS, NUT
- Kungiyoyin NUT da NANS sun fara duba yiwuwar a rufe makarantu a kasar nan
- Hakan na zuwa ne bayan an sace yara kusan 300 a makarantar GSS Jangebe yau
- NANS ta ce Gwamnatin tarayya ta gaza, shugaban NUT ya bada wasu shawarwari
Ganin yadda ake fama da garkuwa da satar yara da ma’aikatan makaranta a wasu bangarorin Najeriya, an kai ga fara maganar a rufe wuraren karatu.
Jaridar Vanguard ta rahoto kungiyar malamai na kasa watau NUT da kuma NANS ta ‘daliban Najeriya, duk su na cewa abin zai kai ga rufe makarantu.
Kungiyoyin sun yi hira da jaridar inda su ka bayyana cewa muddin rayuwar dalibai da malamai su na fuskantar barazana, za su garmake duka makarantu.
Shugaban NUT Dr. Mike Ene, ya ce da alamu akwai wasu da ke kokarin hana yara zuwa makaranta.
KU KARANTA: Yara 317 aka sace a makarantar Jangebe - 'Yan Sanda
Haka zalika shugaban kungiyar NANS na reshen Kudu maso yammacin Najeriya, Kappo Olawale Samuel, ya koka bayan sace yara da aka yi a Zamfara yau.
“Wannan dauke-dauke da ake yi nan-da-can, da gan-gan ne, saboda a cire sha’awar neman ilmi, a kuma jawo yara su yi watsi da karatu.” Inji Dr. Mike Ene.
Shugaban na NUT ya ce ba za su saduda, su ji tsoron barazanar da ‘yan ta’adda su ke yi ba. “Mu na fama da lamarin ‘daliban Kagaram sai kuma ga wannan.”
Ene ya yi kira ga gwamnati ta tsaida manyan katangu domin tsare wadannan makarantu, sannan ya bada shawarar a baza karnuka da ke shinshino masu laifi.
KU KARANTA: Za mu haramta gantali da dabbobi - Nasir El-Rufai
Kappo Olawale a madadin ‘daliban kasar ya ce sun cire rai da gwamnatin tarayya, ya ce ba ta yin abin da ya dace.
NANS za ta kira zama na musamman, daga nan za ta shiga zanga-zanga, har a rufe makarantu. Olawale ya ce matasa ba za su cigaba da kasada da ransu ba.
Dazu kun ji cewa an yi hira da wasu 'yan bindiga a dajin Sabubu, sun fadi abin da ya haddasa rashin zaman lafiya da kuma kashe-kashe a Arewacin Najeriya.
Miyagun ‘Yan bindigan sun fito kiri-kiri a wannan bidiyo, su na cewa ta’adinsu ya fi karfin Gwamnati. Sannan sun yi kira a ba su ilmi, a koya masu abin yi.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng