Gwamnoni da ‘Yan Majalisa su na ba mu kudi, ko Shugaban kasa ba zai iya da mu ba - ‘Yan bindiga

Gwamnoni da ‘Yan Majalisa su na ba mu kudi, ko Shugaban kasa ba zai iya da mu ba - ‘Yan bindiga

- ‘Yan jarida sun yi hira da wasu daga cikin ‘Yan bindigan dake jejin Sububu, Zamfara

- Wani ‘Dan bindiga ya ce rikicinsu ya fi karfin ikon wani Gwamna ko Shugaban kasa

- A cewarsa, an karbe masu shanu, kuma ‘Yan Majalisa ko Gwamna su kan ba su kudi

Jaridar Daily Trust ta yi hira da wani ‘dan bindiga, inda ya yi bayani game da halin da su ke ciki, da yadda gwamnati ta yi watsi da su, da barnar da su ke yi.

Wannan mutumi ya ce gwamnati ta gaza; “Akwai mai, akwai zinari, a albarkatun kasa babu abin da babu (a Najeriya). Amma babu abu guda wanda mu ka san abin da ake yi da shi.”

“Abin da mu ke bukata, yadda su ke daukar ‘ya ‘yansu aiki, su zo su dauki makiyayan nan aiki haka, su sa ‘ya ‘yan (makiyaya) a karatu. Abin da ake yi a kasar, su ma su sani.”

A cewarsa, ba su da abin-yi illa su zo karkashin bishiya su zauna, ya ce an maida su tamkar dabbobi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da 'Yan mata 300 a jihar Zamfara

“Babu dabba, ina wurin kiwo? Sun amshe daji, sun share, babu burtulin da za mu bi. Soja da ‘yan banga da ‘yan bindiga su karbe shanu. Ina ne za a bar mu?”

Game da abin da ya jawo ake rikici da makiyaya, wannan Bawan Allah ya ce rashin karatu ne. “Dukkanmu nan babu wani wanda yake da karatu.”

A jawabin na sa, ya ce babu Makiyayin da yake yin karatu illa na-kusa da wani Minista ko wani babban ma’aikaci mai surukuntaka da shi da ya jawo shi jiki.

Ya ce ko da sun girma, za a iya koya masu karatun zamani da sanin aiki kamar yadda doka ta ce.

KU KARANTA: Boko Haram sun kai wa Fasinjoji hari a hanyar Maiduguri

Bafullatanin makiyayin ya ce yanzu ba su da dabbobi: “Sojoji da jami’an SARS sun karbe shanunmu.

Makiyayin ya ce su na saida shanun da su ka rage masu ne domin su samu kudin kashe wa, ya ce wasu lokutan 'yan Majalisa ko Gwamna kan ba su N100, 000 ko N200, 000.

“Wanga abin da ka ke gani ya fi karfin gwamna, shugaban kasa kan shi idan zai tsaya nan, sai ya nemi taimako daga kasashen waje domin ya iya gyara wannan.”

“Ka duba ka ga mutanen nan duk dauke da makamai, wani an kashe ‘danuwansa, wani har mahaifinsa an kashe. Menene zai iya gyara wadannan mutane?

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel