Rikicin Makiyaya: Matakin da Gwamnonin Arewa za su dauka kwanan nan inji El-Rufai

Rikicin Makiyaya: Matakin da Gwamnonin Arewa za su dauka kwanan nan inji El-Rufai

- Gwamnonin Arewa za su hana Makiyaya gantali su na yawo da dabbobi

- Gwamna Nasir El-Rufai ya ce kan Gwamnonin yankin ya hadu a wannan

- El-Rufai ya na ganin idan an hana dabbobi yawo, za a samu zaman lafiya

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce kungiyar gwamnonin Arewa sun shirya kawo karshen gantalin da ake yi da dabbobi a fadin kasar nan.

Daily Trust ta rahoto gwamnan ya na wannan bayani ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Fubrairu, 2021, sa’ilin da ya zanta da ‘yan jarida a hedikwatar APC.

Gwamnan na Kaduna ya kuma ce sabanin fahimta ya jawo rikici tsakanin gwamnonin Benuwai da na Bauchi, Samuel Ortom da takwaransa, Bala Mohammed.

A jawabinsa, gwamna El-Rufai ya ce kungiyar gwamnonin jihohin Arewa su na kokarin ganin an koma zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a yankin.

KU KARANTA: Yi wa Fulani kudin goro zai iya haddasa yaki in ji El-Rufai

Malam Nasir El-Rufai ya ce yawon da makiyaya su ke yi tsakanin wancan jiha zuwa wancan jiha da dabbobi shi ne babban abin da yake hada su fada da manoma.

“Duk mun shirya magance matsalar yawo sama da kasa da makiyaya su ke yi, domin da zarar an yi maganin wannan, rikicin makiyaya da manoma zai ragu sosai.”

Ya ce: “Kungiyar gwamnonin Arewa ta ci burin hana yawon da dabbbobi da mutane su ke yi a cikin kankannin lokaci, kuma duk mu na aiki (a kan wannan).”

Malam El-Rufai ya tsoma bakinsa kan cacar bakin da ake yi tsakanin gwamna Bala Mohammed na Bauchi, da kuma gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Bauchi ya roki Fulani a kan daukar AK-47

Rikicin Makiyaya: Matakin da Gwamnonin Arewa za su dauka kwanan nan inji El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

“Za a yi maganin matsalar, dole a rika samun banbamcin ra’ayi, amma wannan ba shi ba ne asali.”

A baya mun ji cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya kalubanci Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai da ya kawo hujjar danganta shi da ta'addanci.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Samuel Ortom cikin wani jawabi da ya yi a makon nan, ya yi ikirarin cewa gwamnan na jihar Bauchin dan ta'adda ne mai kare Fulani.

Hadimin gwamnan Bauchi mai taimaka masa a bangaren watsa labarai, Mukhtar Gidado, ya ce mai gidansa ya bukaci Ortom ya kawo hujjoji kan zargin da ya ke yi masa.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel