Bayarabe musulmi bai taba mulkin Nigeria ba tun samun ƴancin kai, MURIC ta koka

Bayarabe musulmi bai taba mulkin Nigeria ba tun samun ƴancin kai, MURIC ta koka

- Kungiyar musulmi ta MURIC, ta koka kan abinda ta kira wariya da ake nuna wa yarbawa musulmi a Nigeria

- Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Ishaq Akintola ya ce tun bayan samun yancin Nigeria ba a taba samun shugaban kasa bayarabe musulmi ba

- Farfesa Akintola ya bada misalai daga jihohi da tarayya inda ake nuna wa musulmi yarbawa wariya wurin nada mukamai a kudu maso yamma

- Daga karshe ya ce lokaci ya yi da ya dace a bawa musulmi bayarabe damar shiga Aso Rock ya kuma nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki

Kungiyar musulunci na kare hakkin bil adama, Muslim Rights Concern, MURIC, ta koka kan cewa babu wani musulmi bayarabe da ya taba zama shugaban Nigeria tun da kasar da samun yancin kai.

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola wanda ya yi wannan koken cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, ya ce an dade ana musgunawa yarbawa musulmi a bangaren siyasa da addini a kasar.

Bayarabe musulmi bai taba mulkin Nigeria ba tun bayan samun yancin kai, MURIC
Bayarabe musulmi bai taba mulkin Nigeria ba tun bayan samun yancin kai, MURIC. Hoto: @TheNationNews
Asali: UGC

A cewar kungiyar ta musuluncin, dukkan shugabannin kasa Yarbawa da suka mulki Nigeria duk Kirista ne.

DUBA WANNAN: FAAC: Jihohi 5 da suka samu kason kudi mafi tsoka a shekarar 2020

Don haka, Akintola, ya yi kira da a samar da shugaban kasa Bayerabe muslmi a 2023, inda ya ce lokaci ya yi da ya kamata a samu hakan idan ana son adalci da dai-daito a kasar.

"An dade ana musgunawa musulmi yarbawa a bangaren siyasa da addini a kasar nan. A kan umurci musulmi masu neman aiki su kawo wasikar daga coci kafin a dauke su aiki.

"A kan raba mukamai daga coci-coci a gwamnati ba tare da la'akari da musulmi ba. Ana nuna wa musulmi Yarbawa wariya wurin nada mukaman siyasa a jihohi da tarayya.

"Misali a mukaman siyasa a jihohin Kudu maso Yamma, ba a yi da musulmi yarbawa, hudu kacal cikin kwamishinonin jihar Oyo da Ogun ne musulmi.

"Abin ya fi muni a Ondo da Ekiti, Gwamna Fayemi ya bawa musulmi kujerun kwamishina biyu kacal cikin 14. Kwamishina musulmi biyu ne kacal gwamnatin Akeredolu kafin ya rushe ta kwanaki biyu da suka shude.

KU KARANTA: Gwamnan Oyo ya amince da hutun sabon shekarar musulunci a jiharsa

"A matakin minista, za mu bada misali da zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Dukkan ministoci shida daga Kudu maso Yamma kirista ne.

"Hakan yasa musulmi yarbawa suka ziyarci tsohon shugaban kasar a Aso Rock inda daga baya ya nada ministoci musulmi biyu cikin shida kafin karshen wa'adinsa," wani sashi na sanarwar.

Don haka MURIC ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar su saka baki don ganin ana yi wa musulmi yarbawa adalci a kasar.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel