'Yan sanda sun kai da ƙafarsu bayan cinna wa ofishinsu wuta

'Yan sanda sun kai da ƙafarsu bayan cinna wa ofishinsu wuta

-Ƙone ofishin ƴan sanda abu ne da ba kasafai ya yake faruwa ba

-Sai dai a wannan karon an samu wasu mutane sun cinna wa ofishin wuta

-Wannan abu ya haifar da firgici ga al'umma sosai dake kusa da wannan ofishi

'Yan sanda sun kai da ƙafarsu bayan kona wa ofishinsu wuta

A samu firgici a jihar Imo a lokacin da ƴan ta-da-zaune-tsaye suka cinna wa hedikwatar ofishin na ƴan sanda wuta na Aboh Mbaise.

KARANTA WANNAN: Mai ba Buhari shawara ya ce AGF ne zai fara kawowa sabon Shugaban EFCC matsala

Saboda haka ƴan sanda suka ranta a na kare a lokacin da masu hargitsin suka fara kwashe wasu kayayyaki daga ofishin na ƴan sanda.

'Yan sanda sun kai da ƙafarsu bayan kuna wa ofishinsu wuta
Ofishin ƴan sanda na ci da wuta. Source: the cable
Asali: Twitter

Daga wata majiya, ƴan ta-da-zaune-tsayen sun iso wajen ne da abubuwan cimma wuta, inda suka fara wurga wa ƴan sandan da kuma sashen gaba ɗaya.

Wannan al'amari ya haifar da firgici a unguwar da ya sanya ƴan sandan gudu sannan su ma sauran mutane suka shige dazuka.

The Punch ta tattara bayanan cewa kusan duk wasu takardu na ofishin ƴan sandan sun ƙone.

Majiyar dai ta cigaba da cewa, "wannan abu ne mai ɗaure kai. ƴan ta-da-zaune-tsayen sun cinna wa ofishin wuta ne tare kuma da kama gabansu ba tare da shiga cikin muhallin mutane ba. Sai kawai suka ɓace abunsu."

KARANTA WANNAN: fitar da 'yan Najeriya 100m daga talauci duk ikirarin siyasa ne, Dr. Ahmed Adamu

"Duk ƴan sanda da kuma waɗanda ke tsare na tuhumar su sun gudu ne cikin dazuka. Sauran mutane ma sun gudu ne gidajensu a lokacin da wutar ta kama. Ba mu taɓa ganin irin haka ba a baya."

Kakakin ƴan sandan da aka tuhuma, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da faruwar lamarin ta hannun mai rahotonmu. A cewarsa, babu wani ɗan sanda da ya rasa ransa a sakamakon al'amarin.

A wani Labarin kuma, Kwamandan Boko Haram Abubakar Shekau ya yi ikirarin cewa shi ya dauka nauyin tashin bama-bamai a Maiduguri a ranar Talata.

A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a yayin harin da 'yan ta'adda suka kai, ganau suka tabbatar.

Wasu mutane 50 sun samu miyagun raunika kamar yadda gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar.

Anas Dansalma ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Sannan marubuci kuma mafassari da ke aiki da Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Online view pixel