Mai ba Buhari shawara ya ce AGF ne zai fara kawowa sabon Shugaban EFCC matsala

Mai ba Buhari shawara ya ce AGF ne zai fara kawowa sabon Shugaban EFCC matsala

- Itse Sagay ya na tsoron alakar da ke tsakanin Malami da shugaban EFCC

- Hadimin Shugaban kasa ya na hangen katsalandan daga ofishin Minista

- Sagay ya ce Malami zai iya kawo tasgaro a yakin da EFCC ta sa a gabanta

Shugaban kwamitin da ke ba shugaban kasa shawara wajen yaki da rashin gaskiya, Farfesa Itse Sagay, ya yi magana a kan nadin sabon shugaban EFCC.

Jaridar Punch ta rahoto Farfesa Itse Sagay SAN ya na cewa Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, zai iya hana Abdulrasheed Bawa yin aikinsa da kyau.

A cewar hadimin na shugaba Muhammadu Buhari, babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, zai rika yi wa sabon shugaban EFCC katsaladan.

Dattijon lauyan ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi hira da shi a ranar Laraba da yamma.

KU KARANTA: Abin da Magu ya fada mani Inji sabon Shugaban EFCC

Itse Sagay ya ce Abubakar Malami ‘dan siyasa ne, don haka bai kamata a kyale shi ya samu ta-cewa a game da aikin EFCC ba, domin hakan zai kawo cikas.

Sagay wanda ‘dan ga-ni-kashe-nin tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu ne, ya ce kutsen da Malami zai yi, zai iya jawo tasgaro a yaki da rashin gaskiya.

Ya ce Malami ya yi kaurin-wuya. “Na lura dukkansu sun fito ne daga jiga guda; Kebbi, watakila ma su na da alaka. A wuri na, wannan ba zaman lafiya ba ne.”

Ya kamata ace shugaban EFCC da kuma hukumar su na cin gashin kansu ne inji Farfesa Sagay.

KU KARANTA: Kungiya ta na so a dawo da binciken da EFCC ta tsaida

Mai ba Buhari shawara ya ce AGF ne zai fara kawowa sabon Shugaban EFCC matsala
Abubakar Malami da Itse Sagay
Asali: Facebook

“Su (EFCC) ba ‘yan siyasa ba ne, jami’an tsaro ne da aka yi wa horo. Babban lauyan gwamnati ‘dan siyasa ne, wanda yake da duk wata nakasa ta ‘dan siyasa.”

Farfesan ya ce Malami ya na da bata-gari a abokansa da zai kare, ya ce wasu su kan shuka barna saboda sun san su ke da AGF, amma ya yaba da aikin Bawa.

Kwanaki mun tattaro maku wasu daga cikin bayanan da su ka fito daga bakin Abdulrasheed Bawa a lokacin da ake tantance shi a matsayin shugaban EFCC.

Abdulrasheed Bawa mai shekara 41 ya ce ya ya shafe shekaru 16 a EFCC, sannan ya samu horo daga hukumar FBI da cibiyar binciken laifuffuka ta kasar Ingila.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng