Damfara: Maina ya fadi babu nauyi, kotu ta soke bukatar belinsa

Damfara: Maina ya fadi babu nauyi, kotu ta soke bukatar belinsa

- Wata babbar kotun tarayya me zama a Abuja ta yi watsi da bukatar belin tsohon shugaban hukumar fansho

- Kotun ta ce Abdulrasheed Maina bai cancanci a bada belinsa ba a karo na biyu duk da ikirarin rashin lafiya da yake

- An damko Maina a jamhuriyar Nijar a watan Disamba bayan da aka bada belinsa ya tsere aka garkame Ndume

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar belin da Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa ya mika gabanta.

Ana shari'ar Maina ne inda ake zarginsa da wawure kudi da suka kai naira biliyan biyu kuma ya daina halartar zaman kotu a watan Satumba, lamarin da ya jefa sanata Ali Ndume gidan gyaran hali.

An kama shi a jamhuriyar Nijar inda ya je neman mafaka kuma aka dawo da shi Najeriya a ranar 3 ga watan Disamban 2020, The Cable ta wallafa.

KU KARANTA: Fatima Atiku ta musanta rade-radin da ake na sabunta rijistarta a APC

Damfara: Maina ya fadi babu nauyi, kotu ta soke bukatar belinsa
Damfara: Maina ya fadi babu nauyi, kotu ta soke bukatar belinsa. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

Daga bisani an kwace belin Maina da aka bada kuma aka bukaci a cigaba da tsaresa a gidan gyaran hali har sai an kammala shari'arsa.

A wata bukata ta ranar 19 ga watan Fabrairu wanda Maina ya mika ta hannun lauyansa Sani Katu, ya bukaci a bada belinsa saboda halin rashin lafiya da yake ciki.

Ya yi ikirarin cewa zai iya rasa kafarsa matukar aka hana shi zuwa neman magani.

A yayin yanke hukunci a ranar Alhamis, alkali Okon Abang ya ce tsohon shugaban hukumar fanshon bai cancanci beli ba.

KU KARANTA: Kagara: Dogo-Gide, shugaban 'yan bindiga ya tuntubi iyayen yara a kan kudin fansa

A wani labari na daban, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce ba zai taba bada hakuri ba a kan tsokacin da yayi a makon da ya gabata ga wadanda ke kwatanta 'yan kabilar Fulani da makasa ko masu garkuwa da mutane.

Idan za a tuna, gwamnan ya fuskanci manyan kalubale tare da caccaka bayan da yace makiyaya na da damar yawo da bindiga kirar AK-47 domin baiwa kansu kariya.

Mohammed wanda yayi jawabi a ranar Laraba yayin kaddamar da kamfen din yi wa dabbobi riga-kafi na 2020/2021 wanda aka yi a Galambi da ke jihar Bauchi.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel