Masu garkuwa ne son a rika biyansu fansa da miyagun kwayoyi, Buba Marwa

Masu garkuwa ne son a rika biyansu fansa da miyagun kwayoyi, Buba Marwa

- Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa y bayyana damuwarsa kan mummunan tasirin da miyagun kwayoyi ke yi a kasar

- A cewarsa Marwa, yanzu masu garkuwa da mutane da bata-gari sun fara neman a biya su kudin fansa da miyagun kwayoyi

- Marwa ya yi kira ga jama'ar Nigeria su bawa hukumar goyon baya da hadin kai domin ganin an magance matsalar ta'amulli da miyagun kwayoyin

Shugaban hukumar yaki da fatauci da ta'amulli da miyagun kwayoyi, NDLEA, Brig. Janar Mohammed Buba Marwa (mai murabus) a ranar Alhamis, ya yi gargadi kan karuwar ta'amulli da miyagun kwayoyi a Nigeria.

A cewarsa, masu garkuwa da mutane da sauran bata gari sun fara neman a biya su fansa da miyagun kwayoyi a maimakon kudi kafin su sako wadanda suka sace.

Masu garkuwa ne son a rika biyansu fansa da miyagun kwayoyi, Buba Marwa
Masu garkuwa ne son a rika biyansu fansa da miyagun kwayoyi, Buba Marwa. @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hotunan auren mace mai shekaru 91 da mijinta mai shekaru 71 da aka daura bayan shekaru 10 suna soyayya

Sanarwar da kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya fitar ta ce Marwa ya nuna damuwarsa kan batun na yayin kaddamar da "kwamitin ayyuka na musamman" na hukumar kan yaki da ta'amulli da miyagun kwayoyi da safarar su.

Ya kuma yi kira ga yan Nigeria su bada gudunmawarsu kan yakin da ta'amulli da miyagun kwayoyi a kasar.

Marwa ya ce amfani da miyagun kwayoyi ya zama annoba ya kai kimanin miliyan 15 don haka ba abin mamaki bane ganin yadda aka samu karuwar miyagun laifuka kamar garkuwa da mutane, ta'addanci, kisan kai, fashi da saransu.

KU KARANTA: Abin da yasa muka tuba muka miƙa makamanmu, tsaffin 'yan bindigan Zamfara

"Duk laifukan na da akaka da shan miyagun kwayoyi. Yanzu miyagu na neman a biya su fansa da miyagun kwayoyi, idan ba mu magance wannan matalsar ba, bata gari za su ta karuwa a kasar.

"Gashi kuma abin baya nuna wa a fuska, amma dukkan mu mun san wani ko wanda ya san wani da ke shan miyagun kwayoyi don haka akwai bukatar mu hada kai a matsayin yan Nigeria don yaki da matsalar," wani sashi na jawabin Marwa.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel