'Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da sace ɗan majalisar jihar Taraba

'Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da sace ɗan majalisar jihar Taraba

-'Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da sace ɗan majalisar jihar Taraba

-Ayyukan garkuwa da mutane abu ne da ke cigaba da ciwa Najeriya tuwo a ƙwarya

-Sai dai ƴan sanda sun yi ƙoƙarin kama waɗanda ake zargi da sace wani ɗan majalisar jiha

-Wannan ƙoƙari dai wataƙila ka iya ƙarfafa wa mutane guiwa kan yaƙin da ake kan yi

Ƴan sanda sun cafke mutane tara da ake zargi da garkuwa da wani ɗan majalisa na Taraba, Mohammed Bape a watan Satumbar da ta gabata.

Waɗanda ake zargin dai an kama su ne a wata maɓoyarsu da ke Taraba da Filato bayan lalube mai tsanani da suka yi.

KARANTA WANNAN: Dillan shanu sun shiga yajin aikin kai kayansu kudu.

Masu garkuwar dai na cikin mutane arba'in da takwas da aka yi wa tonon asiri a ranar Alhamis kamar yadda kakakin rundunar ƴan sandan, CP Frank Mba, ya bayyana.

'Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da sace ɗan majalisar jihar Taraba.
'Yan sanda a bakin fama Source: Premium Times
Asali: UGC

Masu garkuwar sun haɗa da: Yusuf Abubakar, 31; Muntari Umar, 27; Ahmadu Dahiru, 28; Ali Wurungo, 25; Buhari Nuhu, 25; Mohd Garba, 30; Yusuf Jibrillah, 23; Adamu Ahmadu aka Bulala 32 and one Idi Suleiman (shekarunsu ne a jikin sunayensu).

KARANTA WANNAN: Damfara: Maina ya fadi babu nauyi, kotu ta soke bukatar belinsa

Majiyar dai ta cigaba da cewa: "Binciken ƴan sanda ya bayyana cewa masu garkuwar dai na cikin ƙungiyoyin masu fashi da makami da garkuwa da mutane da suke cuzguna wa al'umma a jihohin Filato da Taraba."

Binciken ya bayyana irin rawar da kowa ya taka a yayin wannan mummunan aiki da yadda aka kasafta wa kowa laifinsa.

Ƴan sanda sun ce sun yi nasarar samun wasu kayayyaki wacce jami'an Tsaro na Musamman na FIB reshen Operation Puff Adder II.

Ƴan sandan sun bayyana sumun bundigu goma sha huɗu (AK47) da alburusai da na'urar POS da kwamfutoci biyu da wayoyin hannu sha takwas da masuburbuɗar data da katin ATM tara.

A wani bangare guda: Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce Fulani ba ‘yan ta’adda ba ne. Ya fadi haka ne a Abuja jiya yayin ziyarar girmamawa ga ma'aikatan gudanarwa da sauran ma'aikatan Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), Daily Trust ta ruwaito.

Na riga na tsaya a kan wannan; mu ba 'yan ta'adda bane ba kuma masu aikata laifi ba. Tabbas, akwai 'yan ta'adda a tsakaninmu kuma hakan bai sanya dangi ko dukkan musulmai a matsayin masu aikata laifi ko yan ta'adda ba," yace.

Anas Dansalma Anas Dansalma ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Sannan marubuci kuma mafassari da ke aiki da Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai. Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng