Gwamnan Oyo ya amince da hutun sabon shekarar musulunci a jiharsa

Gwamnan Oyo ya amince da hutun sabon shekarar musulunci a jiharsa

- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da hutun sabon shekara na kalandar musulunci

- Gwamnan ya ce ya dauki wannan matakin ne saboda kiraye-kiraye da al'ummar musulmi na jihar suka yi

- Malaman addinin musulunci a jihar Oyo ta sun bayyana cikinsu matuka bisa wannan cigaban da aka samu

Bayan kiraye-kiraye da al'ummar musulmin jihar Oyo suka dade suna yi, Gwamna Seyi Makinde a ranar Laraba ya amince da hutun sabuwar shekarar musulunci domin jama'ar musulmi a jihar, rahoton The Punch.

Gwamnan Oyo ya amince da hutun sabon shekarar musulunci a jiharsa
Gwamnan Oyo ya amince da hutun sabon shekarar musulunci a jiharsa. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan auren mace mai shekaru 91 da mijinta mai shekaru 71 da aka daura bayan shekaru 10 suna soyayya

Makinde, a jawabinsa na ranar Maulidin Annabi (SAW) a gidan gwamnati da ke Agodi, Ibadan, babban birnin jihar, a ranar Laraba ya ce an amince da hutun ne saboda amsa kirar da musulmin jihar suka yi.

Ya ce, "Wasu mutane sun ce Seyi Makinde baya son musulmi su rika bikin Maulidin Annabi. A bara ba mu yi ba, amma da mai bada shawara kan harkokin addinin musulunci ya zo ya same ni wannan shekarar; duk da COVID-19 da wasu dokokin, zai dace mu yi a bana. Don haka na amince."

KU KARANTA: Kotu ta wanke matar da ake zargi da kashe ƴar aikin ta a Kano

Malaman addinin musulunci da suka yi magana a wurin taron sun bayyana farin cikinsu matuka bisa wannan cigaban da aka samu.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel