Kotu ta wanke matar da ake zargi da kashe ƴar aikin ta a Kano

Kotu ta wanke matar da ake zargi da kashe ƴar aikin ta a Kano

- Kotu a jihar Kano ta wanke matar aure, Fatima Hamza da ke zargi da kashe ƴar aikin ta, Khadijah

- Kotun ta saki Fatima Hamza bisa la'akari da rahoton binciken Ma'aikatar Shari'a na jihar da ya ce babu hujjar cewa ita ta aikata laifin

- Don haka kotu tana shawartar yan sanda su sake gudanar da bincike su gayyato wanda abin ya shafa idan an samu mai laifi a gurfanar da shi

Alƙalin kotun Majistare a Kano, a ranar Laraba, ya saki tare da wanke matar aure mai shekaru 30, Fatima Hamza da ake zargi da kashe ƴar aikin ta, Khadijah, 22, a Sharada Quarters, Kano.

Mai Shari'a Ibrahim Khalil ya saki wanda aka yi ƙarar ne bayan rahoton bincike da Ma'aikatar Shari'a na jihar ya gano ba ta da laifi, The Punch ta ruwaito.

Kotu ta wanke matar da ake zargi da kashe ƴar aikin ta a Kano
Kotu ta wanke matar da ake zargi da kashe ƴar aikin ta a Kano. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Khalil ya ce, "Bayan samun shawarwari daga Sashin Binciken Jama'a na Ma'aikatar Shari'a mai ɗauke da kwanan wata ranar 22 ga watan Fabrairu, na jingine rahoton farko na kuma sallami wanda aka yi ƙarar ta."

DUBA WANNAN: Hotunan auren mace mai shekaru 91 da mijinta mai shekaru 71 da aka daura bayan shekaru 10 suna soyayya

Tunda farko, a yayin zaman kotun a ranar Laraba, lauyan mai ƙara M.S. Ahmad, ya gabatar wa kotu shawarar DPP, kamar yadda sashi na 376 (6) da 299 (3) na dokar ACJL 2019 don jingine rahoton farko.

Ahmad ya bukaci kotun ta rufe shari'ar ta sallami wanda ake zargi kamar yadda sashi na 259 (3) 376 (3) na ACJL ya tanada.

"Babu wani hujja da ke nuna wanda aka yi ƙarar ta aikata laifin. Ya kuma kamata a tura wa ƴan sanda shawarar da Ma'aikatar Shari'a ta bada don su yi ingantaccen bincike, su gayyaci wadanda abin ya shafa, idan an same su da laifi a gurfanar da su a kotu," Ahmad ya ƙara cewa.

Lauyan wanda aka yi ƙarar, Ibrahim Chedi, shima ya amince da shawarar ta Ma'aikatar Shari'a.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe 18, sun kone gidaje sun sace shanu a Kaduna

Idan za a iya tunawa an gurfanar da Fatima ne a kotu kan zargin kisan kai.

An yi zargin cewa a ranar 22 ga watan Janairu ta yi wa ƴar aikin ta (Khadijah) duka sakamakon hakan aka garzaya da ita asibitin ƙwararru na Murtala Mohammad inda likitoci suka tabbatar ta mutu.

Amma, Fatima, ta musanta aikata laifin wanda ya ci karo da sashi na 224 na dokar Penal Code.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel