Kungiya ta tunawa Gwamnatin Buhari wasu Naira Biliyan 900 da aka wawura a gaban idonsa

Kungiya ta tunawa Gwamnatin Buhari wasu Naira Biliyan 900 da aka wawura a gaban idonsa

- Kungiyar HEDA ta ce an yi watsi da wasu binciken satar kudi da aka fara

- HEDA ta rubutawa Shugaban kasa takarda, ta ce an an rasa kusan N900bn

- Wannan kungiya ta na so gwamnatin Buhari ta karbo dukiyar da aka sace

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu rahoton wasu zargin manyan sata 25 da aka tafka, wanda su ka jawo wa gwamnati asarar Naira biliyan 900.

Jaridar Premium Times ta ce kungiyar Human and Environmental Development Agenda (HEDA) ta aika wasika zuwa ga Muhammadu Buhari a makon nan.

Kungiyar HEDA ta yi gargadi cewa ana awon-gaba da kudin al’umma, wanda hakan ya sa ake wasa da yaki da rashin gaskiyar da gwamnatin nan ta ke yi.

Shugaban HEDA, Mr. Suraju Olanrewaju, ya rubuta takarda domin ya farfado da gwamnatin APC, ya ce an yi watsi da zargin satar N900b a gwamnatin Buhari.

KU KARANTA: Bawa ya bayyana dangatakar da ke tsakaninsa da Magu

Daga lokacin da shugaba Buhari ya karbi mulki a 2015 zuwa yanzu, kungiyar HEDA ta ce an manta da binciken zargin satar Naira biliyan 900 da ake yi.

Cikin binciken da aka daina jin labarinsu akwai na Nnamdi Okonkwo wanda EFCC ta cafke a 2015 bisa zargin karbar $115m wajen Mrs. Diezani Alison-Madueke.

Haka zalika an taba kai Dauda Lawal kotu, aka tuhume shi da laifin karbar $25m daga hannun tsohuwar Ministar harkokin man fetur, Diezani Alison-Madueke.

Akwai zargin da aka yi wa marigayi Abdullahi Dikko Inde na cewa ya yi gaba da Naira biliyan 40, haka akwai Jonah Otunla, wanda aka jifa da satar Naira biliyan 2.

Kungiya ta tunawa Gwamnatin Buhari wasu Naira Biliyan 900 da aka wawura a gaban idonsa
Shugaban kasa Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: ‘Dan Majalisar Ajingi/Gaya/Albasu ya kashe N300m wajen gina aji

HEDA ta ce akwai maganar zargin da ke kan Abdulrasheed Maina, da Sanata Danjuma Goje wanda AGF Abubakar Malami ya sa gwamnatin ta yi watsi da su.

Har ila yau, kungiyar ta na so a dawo da maganar zargin da ake yi wa tsohon shugaban hafsun sojan kasa, Tukur Buratai, na mallakar dukiya da gidaje a UAE.

A ranar 24 ga watan Fubrairu, 2021, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana a gaban majalisa, inda aka tabbatar da mukamin da shugaban kasa ya ba shi na shugaban EFCC.

Mun tattaro maku wasu daga cikin bayanan da su ka fito daga bakin Abdulrasheed Bawa a lokacin da ake tantance shi a matsayin sabon shugaban hukumar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng