EFCC: Abubuwa 8 da Abdulrasheed Bawa ya fada da ya bayyana a zauren Majalisa yau
Mun tattaro maku wasu daga cikin bayanan da su ka fito daga bakin Abdulrasheed Bawa a lokacin da ake tantance shi a matsayin shugaban hukumar EFCC.
A yau, 24 ga watan Fubrairu, 2021, Mista Abdulrasheed Bawa, ya bayyana a gaban ‘yan majalisa, ya na sa ran a tabbatar da mukamin da shugaban kasa ya ba shi.
Kamar yadda majalisar dattawan ta bayyana a shafinta na Twitter, Abdulrasheed Bawa ya fara ne da gabatar da kansa, ya karanto takaitaccen tarihinsa a zauren.
“Ina da Digiri da Digirgir daga jami’ar Usmanu Danfodiyo, a jihar Sokoto. Ni kwararren mai binciken masu safarar miyagun kudi ne.” inji Abdulrasheed Bawa.
KU KARANTA: Bawa ya zama sabon Shugaban EFCC
“Na kuma samu horo daga hukumar @FBI da cibiyar binciken laifuffuka a Amurka da Ingila.”
Bawa ya cigaba da bayani: “Na shiga EFCC ne a 2004, aka kuma yi mani horo a matsayin jami’in da ke binciken masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.”
“Ni kadai ne jami’in EFCC da ya rike manyan ofisoshin shiyyoyi uku a tarihi.” Kafin yanzu Bawa ya jagoranci manyan ofisoshin EFCC da ke Fatakwal da Legas.
Bawa ya yi alkawari: “A lokacin da zan bar ofis, zan bar hukumar EFCC fiye da yadda na same ta.”
KU KARANTA: Mai kwankwadar giya ya ke mulkin mutanen Abia – Sanata
A game da sauran takwarori da abokan aikin hukumar a Duniya, Bawa ya ce zai yi aiki da su hannu-da-hannu domin a cin ma buri da manufofin da su ka sa gaba.
“Mu na bukatar mu karbo duk dukiyoyinmu da aka sace domin cigaba da jin dadin ‘yan Najeriya.”
A jawabin Abdulrasheed Bawa, ya yabi EFCC ya ce ita kadai ce hukumar da ta tara mutane daga kowane bangaren kasar nan. Ana sauraron hukuncin da za a dauka.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng