‘Dan Majalisar Kano ya kashe N300m, ya yi wa mutanensa abin da ba za su taba mantawa ba

‘Dan Majalisar Kano ya kashe N300m, ya yi wa mutanensa abin da ba za su taba mantawa ba

- Abdullahi Mahmud Gaya ya kashe N350m wajen gina aji domin a samu wuraren karatu

- Gidauniyar Abdullahi Mahmud Gaya Educational Support ta biya kudin jarrabawar yara

- ‘Dan Majalisar ya kuma kashe miliyoyi ya taimakawa mata da jarin kudi da kayan aiki

Honarabul Abdullahi Mahmud Gaya mai wakiltar mazabar Ajingi, Gaya and Albasu, ya yi wa mutanen da yake wakilta abin da ake sa ran zai amfane su.

Abdullahi Mahmud Gaya ya ce ya kashe sama da Naira miliyan 300 wajen gina aji a makarantun da ke cikin gundumomi 23 daga cikin 30 da yake wakilta.

Vanguard ta ce ‘dan majalisar ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da mutanen mazabarsa.

‘Dan majalisar ya ce ya bada wannan gudumuwa ne domin taimaka wa gwamnati a kokarin da ta ke yi na ganin talaka ya amfana da romon damukaradiyya.

KU KARANTA: Zafin kishin Musulunci ya sa aka fatattake ni daga Jami’ar Kano – Adamu Garba

Abdullahi Gaya yake cewa kadan kenan mutane su ka gani, domin wadanda ayyukan su na kasa.

“A kokarina na gyara sha’anin ilmin boko a mazabata, na iya gina dunkulen aji uku a makarantu 23 daga cikin 30 da su ke karkashin yanki na.” inji Hon. Gaya.

‘Dan majalisar na APC yace wadannan ayyuka duk su na nan, ana jiran kawai a kaddamar da su ne. Gaya ya ce ya kashe N349, 756, 000 wajen wadannan ayyuka,

Ya ce: “Ta karkashin gidauniyar Abdullahi Mahmud Gaya, na biya kudin jarrabawar yaran makaranta na NECO ko WAEC a cikin kananan hukumomi uku.”

KU KARANTA: Buratai su godewa Allah ba mu Majalisa - Shehu Sani

‘Dan Majalisar Kano ya kashe N300m, ya yi wa mutanensa abin da ba za su taba mantawa ba
Abdullahi Gaya Hoto: Daily News
Source: UGC

“Haka zalika mun saye fam mun raba na jarrabawar UTME. Mun kashe fiye da N5,000,000 wajen bada tallafin kudi ga masu karatu a makarantun gaba da sakandare.”

Wajen taimaka wa mata, Gaya ya ce ya ba mata 1,500 jarin N20, 000, inda ya kashe N30, 000, 000, kuma ya raba keken dinki da wasu kayan, sannan ya gina rijiyoyi.

Dazu kun ji cewa jigon APC a Kano, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana amfanin matasa su yi rajista da Jam’iyya, ya ce hakan zai yaki magudin zabe da aka saba yi.

Hon. Ado Doguwa ya musanya rade-radin rikicin cikin gida a jam'iyyar APC, ya ce alamu sun nuna ko da zaben 2023 ya zo, APC za ta doke duk sauran Jam’iyyun.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel