Abin da Magu ya fada mani da Shugaba Buhari ya nada ni Inji sabon Shugaban EFCC

Abin da Magu ya fada mani da Shugaba Buhari ya nada ni Inji sabon Shugaban EFCC

- Abdulrasheed Bawa ya ce akwai alakar kirki tsakaninsa da Ibrahim Magu

- Bawa zai dare kujerar da tsohon Mai gidansa, Magu ya zauna a kai a baya

- Sabon shugaban EFCC yace Magu ya kira shi da aka ba shi wannan mukami

Sabon shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa, Mista Abdulrasheed Bawa, ya yi magana a kan alakarsa da Ibrahim Magu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Abdulrasheed Bawa ya na cewa akwai dangantaka ta mutunci tsakaninsa da tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu.

Abdulrasheed Bawa ya bayyana haka ne yayin Sanatoci su ka tasa shi a gaba, su na yi masa tambayoyi domin a tantance shi a matsayin sabon shugaban EFCC.

Da yake jawabi yau, Abdulrasheed Bawa ya bayyana yadda Magu ya kira shi a waya, ya taya shi murna a lokacin da aka zabe shi a matsayin sabon shugaban hukumar.

KU KARANTA: Abubuwa 8 da Abdulrasheed Bawa ya fada da ya bayyana a zauren Majalisa

“Ina da alaka mai kyau da tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC. Ya kira ni da aka zabe ni, ya yi mani fatan Ubangiji ya ba ni sa’a.” inji Abdulrasheed Bawa.

Jaridar ta ce Sanatocin sun yi wa Bawa tambayoyi a game da yadda ‘yan jarida su ke ruruta labaran ‘yan siyasar da ake bincike da zargin satar kudin al’umma.

Har ila yau, Bawa ya ce EFCC sun yi nasara a fiye da 90% na karar da ta shigar a kotu. Bawa yake cewa EFCC ta yi nasarar daure ‘yan damfara duk da yawan bata lokaci.

Bawa ya yi aiki a karkashin Magu wanda ya kasance mai gidansa a EFCC tsakanin 2016 da 2020. Har ana rade-radin an taba samun sa da aikata ba daidai ba a lokacin.

KU KARANTA: Abdulrasheed Bawa: Wanene Matashin Jami'in da zai rike EFCC

Abin da Magu ya fada mani da Shugaba Buhari ya nada ni Inji sabon Shugaban EFCC
Ibrahim Magu da Abdulrasheed Bawa
Asali: UGC

A tsakiyar shekarar bara ne aka dakatar da Ibrahim Magu daga aiki, sannan aka kuma nada wani kwamiti na musamman da ya yi bincike a kan ayyukan da ya yi a EFCC.

A yau, 24 ga watan Fubrairu, 2021, Mista Abdulrasheed Bawa, ya bayyana a gaban ‘yan majalisa. Kamar yadda ku ka ji, Sanatoci sun tabbatar da Bawa bayan tantacewar.

Bayan wani 'dan lokaci majalisar dattawan ta amince da AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar hana almundahana da yi wa tattalin arziki zagon-kasa.

Shugaban majalisa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya sanar da hakan a zauren majalisar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel