An taba korata a jami'a da karfin tsiya saboda siyasa ina aji 3 – ‘Dan takarar Shugaban kasa

An taba korata a jami'a da karfin tsiya saboda siyasa ina aji 3 – ‘Dan takarar Shugaban kasa

- Adamu Garba II ya ce an taba korarsa daga makaranta a lokacin da yake karatun Digiri

- Tsohon ‘Dan takarar Shugaban kasar ya ce an kore shi ne saboda hana shi takarar SUG

- Garba II ya ce an kore shi ne daga jami’ar fasaha ta Jihar Kano, babu gaira - babu dalili

Tsohon ‘Dan takarar Shugaban kasa a Najeriya, Adamu Garba II, ya bada labarin yadda aka kore shi daga jami’ar fasaha ta Wudil, jihar Kano, shekarun baya.

Malam Adamu Garba II ya ce an jefe shi ne da zargin jawo rigima tsakanin ‘dalibai, aka kore shi daga jami’ar ya na ‘dan aji uku, saboda kurum hana shi takara.

Wannan Bawan Allah mai shekara 38 ya ce abin da ya jawo masa wannan shi ne kiran a ba kowani dalibi damar shiga zaben shugabannin jami’a da ake yi

‘Dan siyasar ya kara shahara ne tun bayan da ya shigar da karar shugaban kamfanin Twitter, ya na neman kotu ta ci shi tara saboda rikicin #EndSARS da yake barke.

KU KARANTA: MACBAN za ta kai Gwamnan Benuwai a kotu saboda kiran Fulani ‘Yan ta’adda’

Ya ce: “Jami’ar jiha ce, kuma na yi suna sosai, amma hukumomin makarantar ba su son ganin wanda ba mutumin jihar Kano ba ya zama shugaban kungiyar dalibai.”

“Ni daga Adamawa na fito, kuma na samu farin jini. Ina takara ne da manufar a ba kowa damar shiga zabe (ba tare da la’akari da addini da kabilarsa ba).” Inji Garba.

A karshe har abin ya jawo aka sallami Garba daga wannan makarantar, bayan ya kai aji uku.

Adamu Garba ya zargi masu ra’ayin rikau na addini da ganin bayansa, yake cewa wannan abin ya faru ne a lokacin da ake tsakiyar kawo tsarin shari’a a jihar ta Kano.

An taba korata ta a jami'a da karfin tsiya saboda siyasa ina aji 3 – ‘Dan takarar Shugaban kasa
Adamu Garba Hoto: @adamugarba
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ba zan koma APC ba, ni ba sa’ansu Marafa da Yari ba ne - Matawalle

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter, Garba II ya ce ya rungumi kaddara, ya bar makarantar, kuma duk da haka ‘dan takararsa ne ya samu lashe zaben.

Dazu kun ji cewa wasu daliban tsangayar ilmin banki a jami'ar Abuja (UniAbuja) sun lallasa malaminsu.

Wadannan 'yan makaranta sun zane wani malaminsu ne saboda ya hanasu cigaba da rubuta jarabawa bayan mintuna 45 da fara jarrabawar da ya kamata ayi sa'a uku.

Da aka tuntubi kakakin kungiyar daliban jami'ar watau SUG, Okuboye Michael Adesina, ya tabbatar da faruwan hakan amma bai da isasshen bayani a kan lamarin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel