2023: ‘Dan Majalisar APC ya cika-baki, mu za mu cigaba da lashe zabe ko a ina aka yi

2023: ‘Dan Majalisar APC ya cika-baki, mu za mu cigaba da lashe zabe ko a ina aka yi

- Alhassan Ado Doguwa ya ce APC za ta yi nasara idan aka gudanar da zaben 2023

- Shugaban masu rinjaye a Majalisar ya ce har yanzu da sauran karfin APC a kasar

- Hon Doguwa yace babu rikicin gidan da ake yi a Jam’iyyar APC ta Kano ko ta kasa

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa ya ce jam’iyyar APC za ta cigaba da mulki a Najeriya har bayan shekarar 2023.

Jaridar Vanguard ta ce ‘dan majalisar na yankin Doguwa da Tudun Wada ya yi wannan cika-baki ne da yake magana kwanaki, ya ce har yanzu da sauransu.

Honarabul Alhassan Doguwa ya ce sakamakon zabukan da aka gudanar a Filato, Legas, Kwara da Neja inda APC ta yi nasara ya nuna irin karfin jam’iyyar.

Jawabin Alhassan Doguwa ya zo ne a lokacin da aka shirya wani taro inda wani abokin aikinsa a majalisa ya yi wa mutanen mazabansa abubuwa na alheri.

KU KARANTA: 'Yan Majalisa 12 da su ka sauya-sheka zuwa APC bayan 2019

A jawabin na sa, Hon. Alhassan Doguwa, ya yi kira ga matasa, manoma da sauran mutane su je su yi rajista da APC, su karbi katinsu na zama ‘ya ‘yan jam’iyya.

‘Dan majalisar ya ce yin rajistar za ta taimaka wajen maganin magudin da ake yi a rumfunan zabe.

“Da wannan rajista, za mu iya gane yawan kuri’un da za mu samu daga kowace rumfar zabe. Mu na kuma so mu zama jam’iyyar da ke da alkalumanta a yanar gizo.”

“Bari in kuma bayyana cewa babu rikici a APC ta Kano da Najeriya.” Doguwa ya cigaba da cewa: Saboda haka ko a Madobi aka yi zabe ko ma ina ne, APC za ta ci.”

KU KARANTA: Ba siyasar 2023 ce a gaba na ba yanzu - Gwamna

2023: ‘Dan Majalisar APC ya cika-baki, mu za mu cigaba da lashe zabe ko a ina aka yi
Alhassan Doguwa Hoto: dailynigerian.com
Source: UGC

“Idan 2023 ta zo, jam’iyyar APC za ta yi nasara, yadda mu ka yi galaba yanzu (a zabukan Filato, Legas, Kwara da Neja), haka za mu sake yin nasara.” Inji Hon. Doguwa.

Reno Omokri ya yi wata hira a jiya, inda ya ce ko da Goodluck Jonathan zai shiga takara, ba zai zabi Gwamna Nasir El-Rufai a matsayin abokin tsayawa takararsa ba.

Na kusa da Goodluck Jonathan din ya hutar da kowa, ya ce tsohon Shugaban kasar ba zai bar PDP ya koma APC ba, sannan ya ce ba zai tsaya takara a zaben 2023 ba.

Tsohon hadimin tsohon shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan, ya karyata jita-itar da ake yi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel