Kungiyar Miyyeti Allah ta na barazanar daina kai dabbobi zuwa Kudancin Najeriya gaba-daya

Kungiyar Miyyeti Allah ta na barazanar daina kai dabbobi zuwa Kudancin Najeriya gaba-daya

- Miyyeti Allah za ta shiga kotu da Samuel Ortom a kan wasu kalamai da ya yi

- Kungiyar ta ce idan Gwamnan bai janye kalamansa ba, za a yi karar sa a kotu

- Makiyayan sun kuma ce za su iya daina kai shanu Kudu idan aka kori Fulani

Kungiyar makiyaya ta Miyyeti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria watau MACBAN ta na barazanar daina kai dabbobbi zuwa kudancin kasar nan.

Miyyeti Allah ta ce za ta umarci makiyayan da ke karkashinta su daina kai wa mutanen yankin Kudu dabbobi, idan har dokar korar Fulani ta cigaba da aiki.

Daily Trust ta ce wannan kungiya ta MACBAN ta reshen jihar Bauchi ta kuma yi barazanar zuwa kotu da Mai girma gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom.

Shugaban kungiyar na Bauchi, Alhaji Abubakar Sadiq, ya ce za su kai gwamnan kotu ne muddin bai janye kalaman da ya yi, ya kira Fulani da ‘yan ta’adda ba.

KU KARANTA: Garkuwa da mutane: Minista ta cirewa Sarki rawani a Abuja

Alhaji Abubakar Sadiq ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da ‘yan jarida a garin Bauchi.

“Idan bai yi maza ya janye kalamansa ba (Samuel Ortom), ba za a bar mu da wata dama ba illa mu tafi kotu, domin mu wanke sunan kabilar Fulani.” Inji Sadiq.

Shugaban na MACBAN ya ce an fara gallaza wa makiyaya a jihar Benuwai ne bayan gwamnan ya kawo dokar da ta haramta yawo da dabbobi a fili, ana kiwo.

“Mutane su yi wa kabilar Fulani adalci, ba za a yi mata kudin goro da cewa marasa gaskiya ba ne. Dole gwamnati ta ba Fulani damar yin sana’arsu babu tsangwama.”

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace Surukar Attajirin Arewa, Dahir Mangal

Kungiyar Miyyeti Allah ta na barazanar daina kai dabbobi zuwa Kudancin Najeriya gaba-daya
Gwamna Ortom Hoto: www.pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

“Mu ma ‘yan kasa ne, dole a dauke mu a matsayin ‘yan Najeriya.” Sadiq yake cewa za a daina ganin dabbobi a Kudu idan aka fatattako makiyaya daga yankin.

A jiya ne mu ka ji cewa wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayinsu a kan da'awar Ahmad Gumi na shiga dajin 'yan bindiga, sannan yana kiran ayi wa miyagun afuwa.

Wadannan mutane da su ka tofa albarkacin bakinsu, sun nemi gwamnati ta gaggauta cafke malamin tare da yi masa tambayoyi a kan harka da 'yan bindigan.

Haka zalika wasu suna ganin malamin yana da kyakkyawar masaniya a kan ta'adin da ake yi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel