Dalibai a jami'ar Abuja sun suburbudi Lakcara yayin zana jarabawa

Dalibai a jami'ar Abuja sun suburbudi Lakcara yayin zana jarabawa

Wasu daliban tsangayar ilmin banki a jami'ar Abuja (UniAbuja) sun lallasa wani malaminsu saboda ya hanasu cigaba da rubuta jarabawa bayan mintuna 45 da farawa duk da cewa sa'o'i uku aka basu.

Jami'ar ta fara rubuta jarabawa ne bayan kimanin shekara guda ana hutu bayan bullar cutar Korona da kuma yajin aikin kungiyar malaman jami'o'i ASUU.

An tattaro cewa daliban na shiga jarabawar da mintuna 45, Malamin yace su dakata kuma sun mika takardunsu.

Hakan bai musu dadi ba, kafin ya ankara wasu cikin daliban suka bi ta kansa, kamar yadda faifan bidiyo ya bayyana.

Yayinda aka tuntubi kakakin kungiyar daliban jami'ar SUG, Okuboye Michael Adesina, ya tabbatar da faruwan hakan amma bai da isasshen bayani kai.

Kalli bidiyon:

Source: Legit.ng

Online view pixel