Saboda tsaron lafiyar jama’a: Za a fara yi wa masu sayar da abinci gwajin lafiya a Kano

Saboda tsaron lafiyar jama’a: Za a fara yi wa masu sayar da abinci gwajin lafiya a Kano

- Hukumar da ke kula da lafiyar abinci da sauran abubuwa a jihar Kano ta ce za a fara yi wa masu siyar da abinci gwajin lafiya

- Za a yi masu gwaji ne a kan cututtuka masu yaduwa kamar tarin fuka, ciwo mai karya garkuwar jikin dan adam da kuma na hanta

- An dauki matakin ne domin tsaftace jihar daga duk wasu gurbatattun abinci domin kiyaye lafiyar al’umma

Hukumar kula da ingancin abinci da sauran abubuwa ta jihar Kano ta bayyana cewa daga yanzu dole ne a rika yi wa masu gidajen abinci gwajin lafiya da sauran cututtukan da ka iya yaduwa kamar su tarin fuka, cuta mai karya garkuwar jiki da na hanta.

Daraktan hukumar, Baffa Babba Dan agundi ne ya bayyana hakan, inda ya ce an dauki matakin ne domin tsaftace jihar daga duk wasu gurbatattun abinci domin kiyaye lafiyar al’umma.

KU KARANTA KUMA: Abun mamaki: Hotunan yarinya ƴar firamare tana gyaran motoci ya jawo cece kuce a yanar Gizo

Saboda tsaron lafiyar jama’a: Za a fara yi wa masu sayar da abinci gwajin lafiya a Kano
Saboda tsaron lafiyar jama’a: Za a fara yi wa masu sayar da abinci gwajin lafiya a Kano Hoto: RFI
Source: UGC

Dan agundi ya kara da cewa duk wanda aka gwada aka ga yana dauke da daya daga cikin wadannan cututtukan za a hana masa sayar da abinci saboda kare lafiyar mutane, shashin Hausa na BBC ya ruwaito.

Hakazalika ya bayyana cewa za a fara wannan gwajin ne daga watan Maris mai zuwa.

Ya kuma jaddada cewa za a rika yin rijistar kyauta, tare da cewa hukumar ba za ta ji nauyin rufe duk wani waje da ya nemi ya yi wasa da wannan doka ba.

KU KARANTA KUMA: Gumi ya koma limamin ƴan bindiga, ya kamata a tuhume shi, cewar wata ƙungiyar Arewa

A wani labari na daban, mun ji cewa manoma a jihar Filato sun caccaki gwamnan jihar Simon Lalong kan zargin da yake musu na mallakar bindigogi kirar AK-47 kamar yadda Fulani makiyaya suke, jaridar Punch ta tattaro.

Lalong ya bayyana haka ne lokacin da yake magana a shirin gidan talabijin na Channels TV, Sunrise Daily a ranar Talata, ya ce ba daidai bane a tasa Fulani makiyaya a gaba kadai ba da zargin mallakar bindigogin AK-47 kasancewar manoma ma suna dashi.

Gwamnan ya ce, “Ba ina bayar da hujjar kowa ya dauki AK-47 bane, amma kar ku manta cewa a yayin gudanar da bincike da kwakkwafi, ba Fulani makiyaya ne kadai ke yawo da AK-47 ba, har ma manoma suma suna da AK-47. ”

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Source: Legit.ng

Online view pixel