Rashin tsaro: Gwamnonin Jihohi na tunanin yin sulhu da ‘Yan bindiga domin a samu zaman lafiya

Rashin tsaro: Gwamnonin Jihohi na tunanin yin sulhu da ‘Yan bindiga domin a samu zaman lafiya

- Kungiyar NGF ta tada tawaga zuwa jihar Neja bayan abubuwan da su ka faru

- NGF na goyon bayan a nemi sulhu da ‘Yan bindiga saboda samun zaman lafiya

- Gwamnan Neja ya ce idan har za a sasanta, a zauna da tubabbun ‘Yan bindiga

Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa kungiyar gwamnonin Najeriya za ta iya yin sulhu da miyagun ‘yan bindiga da nufin kawo zaman lafiya a kasar nan.

Jaridar Punch ta ce shugaban NGF, Dr. Kayode Fayemi ya nuna yiwuwar yin hakan ne a ranar Talata, bayan ya kai wa gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ziyara.

Gwamna Kayode Fayemi ya ziyarci abokin aikin na sa ne tare da wasu takwarorinsa a garin Minna. Hakan na zuwa bayan garkuwa da mutanen da aka yi a jihar.

Kayode Fayemi yake fada wa gwamnan Neja cewa: “Duk mun san irin ciwon da ka ke ji a zuciya. Mun kuma san tsoro da dar-dar din da mutanen jihar Neja su ka shiga.”

KU KARANTA: Minista ta cirewa Sarki rawani saboda hannu a 'garkuwa da mutane'

“Wannan ba bakon abu ba ne. Abin da ya faru ya taba faru wa da wasu. Ka na cikin tawagar da ta ke Borno, Katsina Ogun da Oyo.” NGF ta ke yi wa Bello Allah-kyauta.

Fayemi yake cewa bai so a rika yawan koka wa, ya ce wannan ba shi ne aikinsu ba. “Mutanenmu na neman yadda za a bi a kawo karshen wannan tashin hankali ne kawai.”

Ya ce: “Dole kuma mu duba sauran bangarori dabam da aikin da jami’an tsaro su ke yi, idan hakan ya na nufin ayi sulhu. Watakila babu maka wa, dole sai mun yi hakan.”

Gwamnan na Ekiti yake cewa za su yi duk abin da ta kama domin ganin wannan rikici ya zama tarihi. “Sai mun duba abubuwan da su ka fara sababba wannan rikicin.”

KU KARANTA: MACBAN na shirin maka Gwamna a kotu saboda kiran Fulani ‘Yan ta’adda’

Rashin tsaro: Gwamnonin Jihohi na tunanin yin sulhu da ‘Yan bindiga domin a samu zaman lafiya
Shugaban NGF, Gwamna Kayode Fayemi Hoto: @Kfayemi
Asali: Twitter

Da yake jawabi, gwamnan Neja ya ce ya goyi bayan kiran NGF na cewa ayi sulhu, ya ce amma idan har za ayi hakan, a zauna a sasanta ne da tubabbun ‘yan bindigan.

Tawagar NGF ta kunshi gwamna Simon Lalong (Plateau), Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara), Abdullahi Sule (Nasarawa) da gwamna Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto).

A baya kun ji Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya na cewa bai gamsu da matsayar Ahmad Gumi, na cewa gwamnatin tarayya ta zauna teburin sasanci da miyagu ba.

Gwamnan na Jihar Kaduna, ya ce ba'a sulhu da 'yan ta'adda kuma bai yarda a yi musu afuwa ba.

Kwanan nan an ji gwamnan ya maimaita cewa: "Ban yarda da wannan ba, miyagun ‘yan bindiga ne, mafi yawancinsu a jeji su ke, mu gano su, mu je mu yi maganinsu.”

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel