Rashin tsaro: Gwamna El-Rufai ya yi kaca-kaca da shawarar da Atiku ya ba Buhari

Rashin tsaro: Gwamna El-Rufai ya yi kaca-kaca da shawarar da Atiku ya ba Buhari

- Ra’ayin Gwamna Nasir El-Rufai ya sha banbam da na Atiku Abubakar

- Atiku ya bada shawara a tura Sojoji su tsare duka makarantun Najeriya

- Gwamnan ya yi watsi da wannan shawarar, ya ce ba mai bullewa ba ce

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana game da shawarar da Atiku Abubakar ya bada na aika sojoji domin su tsare dalibai a Najeriya.

Malam Nasir El-Rufai ya yi kaca-kaca da shawarar da aka ba gwamnati, ya ce Najeriya ba ta da karfin da za ta iya kai sojoji zuwa kowace makaranta.

Kamar yadda JJ Omojuwa ya wallafa a shafinsa na Twitter, Gwamnan ya bayyana haka ne a wani bidiyo inda aka yi masa tambaya game da lamarin tsaron.

Ya ce: “Ba mu da isassun jami’an tsaro, ina ganin zai fi kyau muyi amfani da kayan yakinmu wajen maganin miyagun da akasari su ke kungurmin jeji.”

KU KARANTA: Boko Haram sun yi ta’adi a Borno, sun yanka IDP 5

“Sai mun jira sun zo makarantu sun kama ‘ya ‘yanmu? Sojoji nawa za ka baza a makarantu su tsare ‘yan bindiga 200 da za su zo a lokaci daya su kai hari?”

“Sojoji nawa gare mu? Jami’ai nawa za su rika aiki a Arewa maso gabas da Arewa maso yamma, nawa za ka kai jihar Kaduna inda mu ke da makarantu 300.”

Ba zai yiwu ba. Wasu su na ganin wannan matsalar rashin tsaro dama ce da za su ci da siyasa, su rika kawo shirman shawarwarin da ba za su kai ko ina ba.”

"Ban yarda da wannan ba, miyagun ‘yan bindiga ne, marasa gaskiya ne, wanda mafi yawancinsu su ke jeji, mu gano su, mu je mu yi maganinsu.” Inji El-Rufai.

KU KARANTA: Akwai wadanda Allah ya yi wa gyadar doguwa a harin Kagara

Rashin tsaro: Gwamna El-Rufai ya yi kaca-kaca da shawarar da Atiku ya ba Buhari
Gwamna Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

Gwamnan yake cewa bayan an lallasa mafi yawan ‘yan bindigan, za a iya zama da ragowar da su ka tuba, sai ayi masu afuwa, kamar yadda wasu ke fada.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya na goyon matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na wasu daga cikin kadarorin da ta mallaka.

A jawabin da Atiku Abubakar ya yi wa take da: ‘Privatisation of Refineries and Other Assets: Better Late Than Never’, ya ba gwamnatin kasar wasu shawarwari.

Atiku Abubakar ya bayyana wannan ne a wani dogon bayani da ya yi a shafinsa na Twitter a jiya.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng