Ba a sulhu da ƴan ta'adda: El-Rufai ya maida wa Sheikh Gumi martani

Ba a sulhu da ƴan ta'adda: El-Rufai ya maida wa Sheikh Gumi martani

- Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna, ya ce ba'a sulhu da 'yan ta'adda kuma bai yarda a yi musu afuwa ba

- El-Rufai ya fadi hakan ne a matsayin martani ga babban Malamin addini, Sheik Ahmad Gumi

- A baya bayan nan Sheikh Gumi ya gana da wasu daga cikin yan ta'addan da ke zama a dazuzzukan Zamfara

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce bai gamsu da matsayar Ahmad Gumi, babban malamin Addinin Musulunci, na cewa gwamnatin tarayya ta zauna teburin sasanci da yan ta'adda ba, mai makon yin fito na fito da su.

A baya bayan nan Gumi ya gana da wasu daga cikin yan ta'addan da ke zama a dazuzzukan jihar Zamfara, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Bayan ganawar ta su, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da kasafin da ake ware wa fannin tsaro wajen biyan bukatun yan ta'addan, yana mai ikirarin cewa da yawa daga cikin yan ta'addan sun rasa dukkanin wasu kadadori na su ga barayin shanu da sauran iftila'i na rayuwa.

KARANTA: Kurilla: 'Yan Nigeria sun hango kurakurai biyu a jikin sabon katin APC na Tinubu

Amma da ya ke tattaunawa da BBC Hausa a ranar Litinin, El-Rufai ya ce wannan shawara ta Gumi ba za ta haifar da ɗa mai ido ba.

Ba'a sulhu da 'yan ta'adda, a bar batun yi musu afuwa; El-Rufa'i ya mayar wa Sheikh Gumi martani
Ba'a sulhu da 'yan ta'adda, a bar batun yi musu afuwa; El-Rufa'i ya mayar wa Sheikh Gumi martani
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce yan ta'addan ba za su iya daina garkuwa da mutane ba la'akari da irin makudan kudaden da su ke samu.

KARANTA: Abuja: 'Yan bindiga sun shiga har gida sun yi awon gaba da tsohon ACG NIS, Ibrahim Idris, da iyalinsa

"Duk wanda ke tunanin cewa Bafullatanin da ke harkar garkuwa da mutane, yana samun sama da miliyoyi a matsayin kudin fansa, ace zai bar wannan harkar, ya koma rayuwarsa ta baya, ta sayar da shanu akan N100,000, to lallai ya yi wa kansa karya," cewar El-Rufai.

El-Rufai ya kara da cewa rashin hadin kai tsakanin gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma ne ya ƙara rura wutar ta'addanci a shiyyar.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya karbi bakuncin wata tawagar da ta dauki alhakin yin wa'azi domin shiryar da 'yan bindiga.

A jawabin da ya gabatar yayin karbar tawagar, Tambuwal ya sanar da su cewa matsalar tu'ammali da miyagun kwayoyi na kara rura wutar rashin tsaro.

Tambuwal ya bayar da labarin da wani gwamna ya bashi dangane da abinda ya faru har ya san cewa matan Fulani na safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel