Mun sha duka da yunwa: Fasinjojin da ƴan bindiga suka sace a Neja sun magantu

Mun sha duka da yunwa: Fasinjojin da ƴan bindiga suka sace a Neja sun magantu

- Wasu daga cikin fasinjojin da yan bindiga suka sace daga motar NSTA a Kauyen Kundu a jihar Niger sun bayyana halin da suka shiga a hannun masu garkuwa

- Maza biyu da suka magantu sun ce sun sha yunwa da suka sannan ruwa mai datti ake basu irin na dabobi ga rashin barci

- A bangaren mata kuma wata mata ta ce kwanansu bakwai ba wanka, ba wanke baki, ba isashen abinci kuma daga baya suma sun sha duka

Fasinjoji NSTA ta jihar Niger da yan bindiga suka yi garkuwa da su sun ce wadanda suka yi garkuwa da su sun wulakanta su a yayin da suke tsare, Vanguard ta ruwaito.

Wadanda abin ya faru da su, a hira da aka yi da su daban-daban tare da kamfanin dillancin labarai, NAN, a Minna ranar Litinin sun ce yan bindigan sun saka su yin tafiya mai tsawo cikin daji yayin da suke jin yunwa ga kuma duka.

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne yan bindigan suka sace fasinjoji 52 a kauyen Kundu da ke karamar hukumar Rijau yayin da suke dawowa daga Minna.

Mun sha duka da yunwa: Fasinjojin da yan bindiga suka sace a Niger sun magantu
Mun sha duka da yunwa: Fasinjojin da yan bindiga suka sace a Niger sun magantu. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Daya daga cikin wadanda aka sace, Mohammed Ndagi, ma'aikacin gwamnati a hukumar Kimiyya da Fasaha ta jiha ya ce yan bindigan sun tare motarsu misalin karfe 2.30 na rana kuma kafin motar ta tsaya sun harbi motar da bindiga.

DUBA WANNAN: Saurayina mai yara 6 ya bani bindigar kuma ina kungiyar asiri, Dalibar da ta kai bindiga makaranta

Ya ce yan bindigan sun umurce da su sako daga motar suka kuma tisa keyarsu zuwa cikin daji inda suka rika tafiya dare da rana.

"Mata da yara kawai yan bindigan suka dauka a babur zuwa wani wuri.

"Da muka taka zuwa wurin da matan suke, dare ya yi, sun dafa taliya suka zuba mana a hannun mu domin mu ci.

"Mu ke wa kanmu girki a kullum kuma suka cigaba da dukan mu a lokacin da muke tafiya, muna ta ganin sabbin yan bindigan," in ji shi.

Wani da aka sace, Hamza Mohammed, shima ya ce sun sha wahala wurin yan bindigan.

Ya ce cikin jarkar ruwa mai dauda da ake bawa shanu ruwa aka basu ruwa su 10.

"Ranar farko, mun huta a kan dutse kuma duk wanda ya fara barci sai a tashe shi da bulala," in ji shi.

KU KARANTA: Matar aure na neman saki saboda mijinta ya 'kasa yi mata ciki'

Ya ce ranar da aka sako su yan bindigan sun roke su su yafe musu duk abinda suka yi musu sannan su musu addu'a su sauya halayensu.

Kazalika, Hajiya Jummai Isah, daya daga cikin wadanda aka sace, tace hankalinta ya tashi sakamakon halin da ta shiga a hannun yan bindigan.

Ta ce ba suyi wanka ba na tsawon sati daya kuma basu wanke baki ba, sannan abincin da ake ba su baya isa.

Amma ta ce yan bindigan ba su barin mata da yara su taka a kafa, su kan dauke su a kan babur.

Ta ce ba su dukan matan sai dai da ya rage saura kwanaki uku a sako su ne aka fara dukan mata da cewa mutanensu sun ki biyan kudi.

Isah ya mika godiyarsa ga gwamnatin tarayya da na jiha bisa kokarin da suka yi na ceto su da sada su da yan uwansu.

A bangarensa, Gwamna Abubakar Sani-Bello na Niger yayin ganawa da wadanda aka yi garkuwar kafin sada su da iyalansu ya bukaci su kwantar da hankulansu su cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel