GSS Kagara: Abin da yasa soji ba za su yi fito-na-fito da ƴan bindaga ba, Tsohon direkta a DSS

GSS Kagara: Abin da yasa soji ba za su yi fito-na-fito da ƴan bindaga ba, Tsohon direkta a DSS

- Tsohon mataimakin direkta na DSS ya yi fashin baki kan dalilin da yasa sojoji ba za su yi fito-na-fito da yan bindiga ba

- Mr Dennis Amachree ya ce sojojin ba su son a salwantar da rayyukan wadanda aka yi garkuwar da su ne shi yasa suke nazari

- Amachree ya ce yan bindigan suna iya amfani da daliban da suka sace a matsayin garkuwa idan sojojin sun afka musu da harbe-harbe

Tsohon mataimakin direkta a hukumar yan sandan farar hula, DSS, Mr Dennis Amachree, ya ce sojojin Nigeria ba za su yi fito na fito da yan bindiga ba saboda gudun yi wa wadanda aka yi garkuwa da su lahani, rahoton The Punch.

Ya bayyana hakan ne a shirin Sunrise Daily da aka yi Channels Television a ranar Litinin 22 ga watan Fabrairun 2021.

GSS Kagara: Abin da yasa sojoji ba za su afka wa yan bindiga ba, Tsohon direkta a DSS
GSS Kagara: Abin da yasa sojoji ba za su afka wa yan bindiga ba, Tsohon direkta a DSS. Hoto: Premium Times
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Matar aure na neman saki saboda mijinta ya 'kasa yi mata ciki'

Yan bindigan sun sace dalibai da ma'akata a Kwallejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara a jihar Niger.

Yan bindigan, a safiyar ranar Laraba sun kai hari kwallejin, inda suka hallaka dalibi daya sannan suka sace wasu daliban da malamai.

Amachree ya ce, "Idan kaga yan bindiga da yawa hakan, za ka yanke shawarar ko zaka nemi karin jami'ai ko zaka afka musu. Na biyu, wasu lokutan suna tare da wadanda suka yi garkuwa da su kuma suna iya amfani da su a matsayin garkuwa."

DUBA WANNAN: Saurayina mai yara 6 ya bani bindigar kuma ina kungiyar asiri, Dalibar da ta kai bindiga makaranta

Tsohon shugaban na DSS ya kuma bayyana damuwarsa kan irin matakan tsaro da ake saka wa a makarantu ciki har da kwallejin Kagara.

Ya ce babu katanga da ta zagaye makarantar, sai dai kofar shiga kawai kuma gine-ginen duk suna zube wa.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel