Ainihin abin da ya hana ‘Yan bindiga su fito da ‘Yan makaranta da ma’aikatan da aka sace a Neja

Ainihin abin da ya hana ‘Yan bindiga su fito da ‘Yan makaranta da ma’aikatan da aka sace a Neja

- Har zuwa yanzu mutanen da aka sace daga GSSS Kagara su na nan a tsare

- Rahotanni sun ce an samu rashin jituwa tsakanin bangarorin ‘Yan bindigan

Akwai alamu da ke nuna cewa an samu sabani tsakanin ‘yan bindigan jihar Neja, wanda hakan ya hana a fito da yara da ma’aikatan da aka sace a garin Kagara.

Punch ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 22 ga watan Fubrairu, 2021, ta ce wannan sabani da aka samu ne ya yi sanadiyyar jinkiri wajen sakin wadannan mutane.

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa ba a gama shawo kan wadanda su ka dauke dalibai 27 da ma’aikata 15 daga makarantar gwamnatin kwana ta Gagara ba.

An yi sulhu ne ta hannun wani gawurtaccen ‘dan bindiga, shi kuma har yanzu wannan mutumi bai kai ga cin ma yarjejeniya da wadanda su ka dauke mutanen ba.

KU KARANTA: An kusa daina jin labaran kashe-kashe da hare-hare - Ahmad Lawan

A ranar Lahadi aka samu rudani, inda jami’an gwamnatin Neja su ka bada sanarwar an fito da wadannan dalibai da ma’aikata, kuma su na hanyar zuwa Minna.

Daga baya kuma sai aka ji mai girma gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya ce mutanen na tsare.

“Akwai sabani ne tsakanin bangarorin miyagun ‘yan bindigan. Ana lallabar wadanda su ka dauke mutanen, su fito da su.” Inji wani jami’in gwamnati na jihar Neja.

A wata hira da aka yi da Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa ana kokarin shawo kan ‘yan bindigan su fito da mutanen da su ka dauke daga makarantar.

KU KARANTA: Pantami ya bi sahun Sultan, Zulum, ya tashi da kyauta a 2020

Ainihin abin da ya hana ‘Yan bindiga su fito da ‘Yan makaranta da ma’aikatan da aka sace a Neja
Abubakar Sani Bello da IGP Hoto: @Abusbello
Asali: Twitter

Shehin Malami Gumi ya ce: “Su na neman cin ma yarjejeniya tsakaninsu – bata-gari da mugu. Ana neman a shawo kansu, kuma ina sa ran cewa za ayi hakan.”

A makon jiya wani mazaunin garin Kagara ya shaida wa 'yan jarida yadda aka sace dalibai 27 da ma’aikata 15 a makarantar kimiyya ta kwana ta gwamnatin Jiha.

Wannan mutumin da ke zaune kusa da makarantar, ya bayyana wa manema labarai cewa ‘yan bindigan masu dauke da kayan sojoji, sun duro ne cikin tsakar dare.

'Yan bindigan sun ajiye baburansu kusa da wata makarantar sakandiren Attahiru kafin a kai GSS Kagara.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel