Shugaban Majalisa ya hadu da Buhari, ya yi alkawari za a samu zaman lafiya nan da wata 2
- Shugaban Majalisar tarayya ya gana da Shugaban kasa a farkon makon nan
- Ahmad Lawan ya bayyana irin kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya
- Sanatan yace zaman lafiya za ta dawo kasar nan kafin ruwan sama ya sauko
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya bada wa’adin watanni biyu, ya ce zuwa wannan lokaci, za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
The Nation ta ce Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya bada wannan tabbaci ne da yake magana da manema labarai a Aso Villa bayan ya gana da shugaban kasa.
Ahmad Ibrahim Lawan ya hadu da Mai girma Muhammadu Buhari ne a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 22 ga watan Fubrairu, 2021, inda su ka tattauna.
Da yake yi wa ‘yan jarida jawabi a jiyan, shugaban majalisar ya ce Muhammadu Buhari ya na bakin kokari na ganin zaman lafiya da tsaro ya dawo kasar nan.
KU KARANTA: Kungiyoyi sun ce Buhari ya yi murabus idan babu tsaro
Lawan ya ce gwamnati ta na neman kawo karshen kashe-kashen da ake yi kafin damina ta shigo ko manoma su samu damar da za su yi shuka hankali kwance.
A cewar Sanata Lawan, majalisar tarayya za ta yi na ta kokari, ta ba jami’an tsaro gudumuwar da su ke bukata, ta hanyar ware kudi domin a sayo makaman yaki.
“Na zo na gana da shugaban kasa domin muyi magana a kan sha’anin tsaron kasarmu, asali ma babu wani lamari da ya fi wannan muhimmanci yau a Najeriya.”
“Mun yi doguwar tattaunawa a kan batun tsaron duka bangarorin kasar nan, da yadda za a shawo kan lamarin nan, mu na da rawar da za mu taka duka.” Inji Lawan.
KU KARANTA: Boko Haram sun yi wa mutane yankan rago a Damboa
“Dole mu tsare kasa domin mutane su nemi na-abinci. Mu na so manomanmu su koma gona kafin damina ta shigo. Sai an tsare karkara domin a samu lafiya a birane.”
Kwanaki ku ka ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana game da shawarar da Atiku Abubakar ya bada na aika sojoji domin su tsare 'yan makaranta.
Nasir El-Rufai ya caccaki Atiku Abubakar, ya ce wasu ‘yan siyasa su na amfani da rashin tsaro, su rika sakin baki, su na fadan soki-burutsu da sunan bada shawarwari.
El-Rufai yake cewa ba zai yiwu a baza sojoji zuwa kowace makaranta ba, domin babu isassun jami'ai.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng