Attahiru ya ba sojin Najeriya sa'o'i 48 su kwato Marte daga hannun Boko Haram
- Babban hafsin sojin kasa, manjo janar Ibrahim Attahiru ya bai wa rundunar OLD sa'o'i 48 ta kwace garin Marte daga hannun 'yan Boko Haram
- Sannan ya umarcesu da su kwato garin Kirenowa, Kirta, Wulgo, Chikingudo dake karkashin Marte da karamar hukumar Ngala jihar Borno
- Attahiru ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Lahadi yayin da yake yi wa rundunar Nigerian Army Super Camp 9, a Dikwa jawabi
COAS, manjo janar Ibrahim Attahiru ya baiwa rundunar sojin Operation Lafiya Dole sa'o'i 48 da su yi gaggawar kwato Marte daga hannun 'yan Boko Haram sannan su yi gaggawar kwace garuruwa irinsu Kirenowa, Kirta, Wulgo, Chikingudo dake karkashin karamar hukumar Marte da Ngala dake jihar Borno.
Attahiru ya bayar da wannan umarnin ne a ranar Lahadi yayin yi wa sojojin Najeriya na Super Camp 9 jawabi a Dikwa, The Nation ta tabbatar.
Ya tabbatar wa da rundunar cewa lallai yana bukatar su sanya kwazo akan aikin, kuma su yi shi cikin sa'o'i 48.
KU KARANTA: Arangama tsakanin 'yan bindiga da jama'a: Rayuka 3 sun salwanta a Kaduna
"Wurare kamar Marte, Chikingudu, Wulgo Kirenowa da Kirta suna bukatar a kammala ayyukansu cikin sa'o'i 48. Kuma kada ku ji komai don mun tanadi duk wasu hanyoyin baku kwarin guiwa.
"Nayi magana da Theater kwamanda da kuma General Officer Commanding 7 Division, wajibi ne ku tsaya wa kasar nan ku yi abubuwan da suka dace," bisa umarnin Attahiru.
Ya kuma ja kunnen rundunar akan kada su yarda su tsere wa 'yan Boko Haram, inda ya kara maimaita cewa "Kun san yadda suka kai wa mutanen Marte da Dikwa hari, kada ku yarda ya kara faruwa, ku bi mugayen kuma ku kashesu".
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Akwai yuwuwar a sako 'yan bindiga da aka kama saboda yaran makarantan Kagara
A wani labari na daban, shaguna masu tarin yawa da ke kasuwar siyar da safayan kayan motoci da ke titin Jos a yankin Oriapata da ke jihar Kaduna sun babbake sakamakon gobarar da ta tashi.
Duk da har yanzu ba a gano musababin wutar ba da ta tashi a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 'yan kasuwa da mazauna yankin sun tabbatarwa da Channels TV cewa gobarar ta fara ne bayan da wani shago daya ya fara babbaka.
Shugabannin kungiyar 'yan kasuwan masu siyar da bangarorin motocin sun ce gobarar ta yi mummunar barna tunda ta shafi kayan kudi masu tarin yawa.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng