PDP ta gigice bayan Jagororin APC su na kokarin janye mata wasu Gwamnoni 3

PDP ta gigice bayan Jagororin APC su na kokarin janye mata wasu Gwamnoni 3

- Jam’iyyar APC ta na neman karkato da ra’ayin wasu Gwamnonin PDP 3

- Daga cikinsu har da Gwamna Bala Mohammed da kuma Bello Matawalle

- APC ta nemi Gwamnan Enugu ya tashi, amma ya nuna ba zai bar PDP ba

Jaridar Punch ta ce jam’iyyar PDP ta shiga rudu bayan yunkurin da wasu shugabannin APC su ke yi na jawo hankalin gwamnonin ta akalla uku a Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar APC ta na kokarin jawo gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, da takwaransa, Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Haka zalika jaridar ta ce shugabannin APC su na farautar gwamnan Kuros Riba, Dr. Ben Ayade.

Jagororin APC da su ke wannan aiki su ne shugaban rikon-kwarya na jam’iyya, kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, da kuma Gwamna Yahaya Bello.

KU KARANTA: Ba zan bar PDP ba - Gwamna Bala

Wata majiya mai karfi daga jam’iyyar APC mai mulki ta shaida wa jaridar a ranar Lahadi cewa APC ta tuntubi har gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Uguwanyi.

Majiyar ta ce Mai girma Ifeanyi Uguwanyi ya yi watsi da tayin da jam’iyyar APC ta yi masa.

“Uguwanyi ya na yi mana taurin-kai. Burinmu shi ne mu samu gwamnoni akalla uku a Kudu maso gabas. Idan ba mu jawo Uguwanyi ba, za mu karbe Anambra.”

Manyan APC a Zamfara irinsu tsohon gwamna Sanata Ahmed Yariman-Bakura, suna kokarin karkato da ra’ayin Bello Matawalle domin ya sauya-sheka daga PDP.

KU KARANTA: 2023: PDP za ta kwace mulkin Najeriya daga hannun Buhari – Gwamna

PDP ta gigice bayan Jagororin APC su na kokarin janye mata wasu Gwamnoni 3
Ben Ayade ya samu sabani da iyayen gidansa Hoto: www.vanguardngr.com
Source: UGC

Bala Mohammed ya na da kyakkyawar alaka mai kyau da fadar shugaban kasa don haka APC ta ke harinsa, yayin da Ben Ayade ya samu matsala da jam’iyyar PDP.

A karshen makon da ya wuce mu ka ji wasu matasa sun ba takarar Gwamnan Kogi goyon baya domin ganin ya gaji kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Alamu sun nuna cewa a shirye Gwamna Yahaya Bello yake da ya shiga takara a zaben 2023.

Takarar shugaban kasar Bello ta samu gagarumar goyon-baya inda aka kaddamar da Bello Ambassadors Network da ta yi masa alkawarin matasa miliyan 10.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel