Gwamna Bello zai samu mutum miliyan 10 da za su yi masa yakin neman Shugaban kasa

Gwamna Bello zai samu mutum miliyan 10 da za su yi masa yakin neman Shugaban kasa

- An kaddamar da wata kungiya mai suna Bello Ambassadors Network a garin Abuja

- Bello Ambassadors Network ta na fafutuka domin Yahaya Bello ya yi takara a 2023

- Edward Onoja ya bukaci kungiyar BAT ta nemo goyon bayan matasa har miliyan 10

Takarar shugaban kasar Yahaya Bello ta samu gagarumar goyon-baya a ranar Asabar, yayin da aka kaddamar da wata kungiya ta Bello Ambassadors Network.

Jaridar Punch ta ce an kaddamar da wannan kungiya ta matasa ne a babban birnin tarayya Abuja.

Mai girma mataimakin gwamnan jihar Kogi, Mista Edward Onoja, da shugaban ma’aikatan fadar gwamnan Kogi, Abdulkareem Asuku, sun halarci taron da aka yi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sakatariyar gwamnatin jihar Kogi, Folashade Arike-Ayoade, da wasu kusoshin gwamnatin Yahaya Bello sun samu halartar taron.

KU KARANTA: Buhari da Atiku sun yi tarayya a saida matatun mai da kadarorin kasa

Shugaban tafiyar Bello Ambassadors Network a fadin Najeriya, Anthony Edogbo, ya yabi gwamna Yahaya Bello da ya karbi wannan kungiya, ya kuma mara masu baya.

Anthony Edogbo ya ce: “Mun mara baya ne saboda tsananin bukatar a tafiya matasa, da kuma goyon-bayan na mu, Yahaya Bello, shiyasa duk mu ke zaune a yau.”

“Ina da shirin samun mutane miliyan biyar a Disamban 2021, sannan mu kai sakon wayar da kanmu zuwa kyauren kowane gida saboda shekarar 2023.” Inji Edogbo.

Ya ce: “Najeriya kasa ce da adadin matasa ya kai miliyan 33. Amma abin takaici, a shekarun nan, ba mu yi amfani da damarmu da dabararmu da kuma karfinmu ba.”

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun saki tsohon Gwamnan jihar Imo

Gwamna Bello zai samu mutum miliyan 10 da za su yi masa yakin neman Shugaban kasa
Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Edward Onoja ya yi jawabi wajen taron, ya ce a shirye Bello yake ya yi takara saboda matasa, sannan ya yi kira ga BAN su nemi goyon-bayan matasa har miliyan 10.

Dazu kun ji cewa SWAT23 ta ziyarci Sarkin yakin zaben Atiku a 2019, Gbenga Daniel da wani basarake domin su mara wa Asiwaju Bola Tinubu baya a zabe mai zuwa.

Manyan ‘Yan siyasan Yarbawa a karkashin Sanata Dayo Adeyeye sun ce babu wanda ya dace ya gaji kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023 irin Bola Tinubu.

Shugaban SWAGA 23, Dayo Adeyeye, ya kai yakin zabensu zuwa Ogun bayan bude ofis a Oyo da Osun.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel