Matar aure na neman saki saboda mijinta ya 'kasa yi mata ciki'

Matar aure na neman saki saboda mijinta ya 'kasa yi mata ciki'

- Wata matar aure a garin Kaduna ta yi karar mijinta a kotu tana neman a raba aurensu domin baya haihuwa

- Matar, Marwanatu Muhammad ta ce a shirye ta ke ta mayarwa mijinta, Iliyasu, N20,000 da ya biya sadakinta shekaru 10 da suka wuce

- A bangarensa, mijin, Iliyasu, ya ce yana bin Murwanatu bashin kudi N17,000 kuma ya nemi ta biya shi kafin su rabu

Wata matar aure, Marwanatu Muhammad a ranar Litinin ta roki kotun Shari'a da ke zamanta a Rigasa Kaduna, ta raba aurenta da mijinta Iliyasu kan cewa ya gaza yi mata ciki, The Nation ta ruwaito.

A karar da ta shigar, Marwanatu, ta yi ikirarin cewa Iliyasu ya gaza yi mata ciki tunda suka yi aure shekaru 10 da suka shude a 2011.

DUBA WANNAN: Saurayina mai yara 6 ya bani bindigar kuma ina kungiyar asiri, Dalibar da ta kai bindiga makaranta

Matar aure ta nemi kotu ta raba aurenta don mijinta baya haihuwa
Matar aure ta nemi kotu ta raba aurenta don mijinta baya haihuwa. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

"Ya taba yin aure a baya amma matarsa ta rabu da shi saboda baya haihuwa. Ina tunanin nawa zai banbanta amma ashe kuskure na yi,

"Lafiya ta kalau ba ni da matsala. Bana ra'ayin cigaba da zaman auren. A shirye na ke in mayar masa kudin sadakinsa, N20,000," in ji ta.

KU KARANTA: Allah ya yi wa sarki mai sanda mai daraja ta ɗaya rasuwa a Kwara

A bangarensa, Iliyasu ya ce yana bin wacce ta yi karar bashin N17,000 kuma yana son kotu ta taimaka ta karbo masa bashin.

Tunda farko, Alkalin kotun Mallam Salisu Abubakar-Tureta ya umurci ma'auratan biyu su tafi asibiti a musu gwaji domin gano inda matsalar ya ke.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel