Matukin jirgi ya yi korafin matsala a injin sa'o'i kadan kafin ya rikito daga sama

Matukin jirgi ya yi korafin matsala a injin sa'o'i kadan kafin ya rikito daga sama

- Matukin jirgin sama da ya fado a Abuja a ranar Lahadi yayi korafin matsala a injin

- Ya sanar da asamun matsalar ne amma bayan sa'o'i kadan jirgin ya fado warwas

- Tun bayan sace yaran makaranta na Kagara ake ta kaiwa da kawowa zuwa Minna

Matukin jirgin sojan sama na rundunar dakarun sojin sama da ya fadi a Abuja a ranar lahadi, ya yi korafin cewa injin jirgin yana da matsala kafin mintoci kadan da tashin shi.

Wata majiya ta sanar da hakan ga jaridar The Punch amma ya bukaci a adana sunansa.

Jami'in ya ce ana ta samun masu kaiwa da kawowa a jiragen sama daga Abuja zuwa Minna tun bayan sace yara da ma'aikatan makaranta a Kagara a makon jiya.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Akwai yuwuwar a sako 'yan bindiga da aka kama saboda yaran makarantan Kagara

Matukin jirgi ya yi korafin matsala a injin sa'o'i kadan kafin ya rikito daga sama
Matukin jirgi ya yi korafin matsala a injin sa'o'i kadan kafin ya rikito daga sama. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Majiyar ta ce, "Jirgin yana kan hanyarsa ta zuwa Minna. Bayan kankanin lokaci da isarsa karamar hukumar Bassa, ya sanar da cewa injin jirgin ya samu matsala.

"An shawarcesa da ya koma filin sauka da tashin jiragen sama da ke Abuja amma sai ya rikito daga sama."

A yayin da aka bukaci sanin wadanda ke jirgin, jami'in ya ce suna bincikowa.

"Ana ta samun kaiwa da kawowa zuwa jihar Neja tun bayan sace yaran makaranta. A makon da ya gabata ne ministoci suka je har garin. Nan babu dadewa za a gano su waye," yace.

KU KARANTA: COVID-19: Daga bisani, El-Rufai ya amince a bude dukkan makarantu

A wani labari na daban, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a jiya ya ce 'yan kasa basu bukatar izinin takwaransa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, domin zama a dajikan jihohin kudu masu yamma.

Gwamnan jihar Bauchi wanda yayi jawabi a wani shirin gidan talabijin, a bayyane yake magana ga Akeredolu wanda ya bukaci makiyaya su bar dajikan.

Gwamnan ya kara da cewa 'yan Najeriya basu bukatar izinin kowanne gwamna idan za su yada zango a kowacce jiha a cikin kasar nan, ThisDay ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel