Yanzu-yanzu: Akwai yuwuwar a sako 'yan bindiga da aka kama saboda yaran makarantan Kagara

Yanzu-yanzu: Akwai yuwuwar a sako 'yan bindiga da aka kama saboda yaran makarantan Kagara

- Rahotanni da suka samu sun nuna cewa na cigaba da sasanci da 'yan bindiga domin su sako yaran makarantar Kagara

- Akwai yuwuwar gwamnati ta sako wasu 'yan bindiga da ke hannun jami'an tsaro saboda a sako yaran makarantar

- Babban malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai

Rahotanni na nuna cewa za a saki wasu daga cikin 'yan bindigan da ke hannun hukuma a matsayin wani bangaren na yarjejeniyar sako yaran makarantar Kagara da ma'aikatan da aka yi garkuwa da su.

Kamar yadda The Punch ta wallafa, 'yan bindigan da suka sace yaran suna bukatar a sakar musu 'yan uwansu da ke hannun jami'an tsaro kafin su sako yaran.

Fitaccen malamin nan na addinin Islama mazaunin Kaduna, Ahmad Gumi ya sanar a ranar Juma'a cewa ya samu ganawa da 'yan bindigan jihar Neja a cikin kokarinsu na karbo wadanda aka sace.

KU KARANTA: A bar 'yan Najeriya su dinga yawo da makamai idan makiyaya suna yi, Fani-Kayode

Yanzu-yanzu: Akwai yuwuwar a sako 'yan bindiga da aka kama saboda yaran makarantan Kagara
Yanzu-yanzu: Akwai yuwuwar a sako 'yan bindiga da aka kama saboda yaran makarantan Kagara. Hoto daga @dawisu
Asali: Twitter

A yayin jawabi a kan abinda 'yan bindigan ke bukata kafin su saki yaran, Gumi ya ce: "Basu bada takamaiman sharadin da zai sa su saki daliban ba. Muna ta dai rokonsu da su sako su amma sun ce za su sako su.

"Mun gano cewa suna son a sako mutanensu da aka kama kafin su sako wadanda ke hannunsu."

KU KARANTA: Zan iya rasa kafata idan aka hana ni beli, Maina ya sanar da kotu

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode ya sanar da gwamnatin tarayya da ta bar 'yan Najeriya su dinga daukar makamai idan har ta bar Fulani suna yawo da AK47 domin kare kansu da shanunsu.

Kamar yadda yace, idan aka duba lamarin ta haka toh dole ne a baiwa jama'a damar yawo da makamai domin bai wa kansu kariya daga 'yan bindiga da kuma makiyayan, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce hanyar da ta fi dacewa wurin shawo kan matsalar tsaron kasar nan shine dukkan matakai na gwamnati su hada karfi da karfe kuma a hana 'yan Najeriya yawo da makamai.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng