El-Rufai: Yadda za a fatattaki tsofaffi ire-irena daga siyasa

El-Rufai: Yadda za a fatattaki tsofaffi ire-irena daga siyasa

- Gwamna Nasir El-Rufai ya baiwa matasa dabarun da za su yi amfani dasu wurin fatattakar tsofaffi irinsa daga siyasa

- A wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Juma'a, ya yi kira ga matasa, masana da shugabannin addini da su taru su baiwa kasa gudunmawa

- El-Rufai yace zanga-zanga da tada zaune tsaye ba zai taba haifar da da mai ido ba har sai mutanen kirki sun bayyana kawunansu don taimakon kasa

Gwamna Nasir El-Rufai ya baiwa matasa shawarwari da dabarun da za su fatattaki tsofaffi irinsa daga siyasa.

A wata tattaunawa da 'Radio Now's Urgent Conversation' dake jihar Legas suka yi dashi a ranar Juma'a, ya yi kira ga matasa, kwararru a fannoni daban-daban da kuma shugabannin addini da su hada kawunansu wurin ciyar da siyasa da kasar nan gaba.

El-Rufai ya ce zanga-zanga da tayar da hankula ba za su kai kowa ko ina ba har sai mutanen kirki sun taru sun mika kawunansu ga taimakon kasarsu ta gado, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Zan iya rasa kafata idan aka hana ni beli, Maina ya sanar da kotu

El-Rufai: Yadda za a fatattaki tsofaffi ire-irena daga siyasa
El-Rufai: Yadda za a fatattaki tsofaffi ire-irena daga siyasa. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

A cewarsa, "Wajibi ne mutanen kirki su gabatar da kawunansu don yi wa al'umma ayyuka kuma su fuskanci kalubale iri-iri na yau da kullum.

"Za a zagesu, a ci zarafinsu, a kuma zargesu amma duk da haka jajirce su rike kujerun gwamnati don taimaka wa mutanenmu a siyasa, ba a bankuna kadai ake bukatarsu ba, ko kamfanonin sadarwa, kamfanonin mai da sauransu ba.

"Zanga-zanga ba za ta haifar da da mai ido ba, wajibi ne mu zauna mu tattauna a harkokin siyasa."

A cewar El-Rufai, "Na shiga gwamnati ne ta dabara, ban shiga siyasa don a zabeni a matsayin minista ba. Na shiga siyasa ne saboda shugaban kasa yana sona kuma yana kyautata zaton zan iya aiki tukuru. Bayan nan ne na fahimci cewa siyasa babban al'amari ne kuma ta shafi komai ma.

"Don haka ina kira ga 'yan Najeriya matukar suna so siyasa ta inganta, wajibi ne su shiga dumu-dumu a dama dasu. Ka shiga jam'iyya wacce kake ganin zaka iya taimako ta ita, don idan ba ta haka ba, babu wata hanya."

KU KARANTA: Da duminsa: Saraki da jiga-jigan PDP sun yi ganawar sirri da IBB, Abdulsalami

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode ya sanar da gwamnatin tarayya da ta bar 'yan Najeriya su dinga daukar makamai idan har ta bar Fulani suna yawo da AK47 domin kare kansu da shanunsu.

Kamar yadda yace, idan aka duba lamarin ta haka toh dole ne a baiwa jama'a damar yawo da makamai domin bai wa kansu kariya daga 'yan bindiga da kuma makiyayan, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce hanyar da ta fi dacewa wurin shawo kan matsalar tsaron kasar nan shine dukkan matakai na gwamnati su hada karfi da karfe kuma a hana 'yan Najeriya yawo da makamai.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng