Manyan attajirai biyar 'yan arewa daga cikin masu kudin Najeriya na shekarar 2019
A yayin da manyan jaridun duniya suka fitar da jerin sunayen mashahuran masu kudi na shekarar 2019, sannan jaridu a cikin gida suka bayyana manyan hamshakan masu kudi a Najeriya a 2019, Legit.ng ta tsamo wasu 'yan arewa dake cikin attajiran Najeriya.
Ga dan takaitaccen bayani a kan biyar daga cikin masu kudi a Najeriya na shekarar 2019 da suka fito daga yankin arewa.
1. Aliko Dangote
Aliko Dangote, haifaffen jihar Kano, ya kasance bakin mutum mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Aliko ya mallaki kamfanonin rukunin hadakar Dangote dake da rassa da cibiyoyi a kasashen nahiyar Afrika.
A shekarar 2014 ne Dangote ya zama na 23 a cikin masu kudin duniya.
2. Abdulsamad Rabiu
An haifi Abdulsamad Rabiu a cikin arziki, amma duk da haka ya yi kokari wajen mayar da miliyoyin da ya fara kasuwanci da su zuwa biliyoyi.
Mahaifinsa, marigayi Khalifah Isyaku Rabiu, yana daya daga cikin manyan malamai da kuma 'yan kasuwa dake da masana'antu tun a shekarun 1970s da 1980s.
Abdul Samad ne ya kafa kuma yake jagorantar rukunin kamfanonin BUA dake sarrafa kayan abinci da harkokin noma da aiyukan raya kasa. Rukunin kamfanoni da masana'antun BUA na samun ribar da ta kai biliyan $2.5 a shekara.
3. Theophilus Danjuma
Janar Theophilus Yakubu Danjuma, wanda aka fi kira da T. Y Danjuma, tsohon soja da rikide zuwa dan kasuwa kuma dan siyasa.
Ya rike mukamin babban hafsan rundunar tsaro ta kasa daga shekarar 1975 zuwa 1979 kafin daga bisani ya rike mukamin ministan tsaro a gwamnatin mulkin soja ta tsohon shugaban kasa, janar Olusegun Obasanjo mai (ritaya).
Yanzu haka shine shugabann kamfanin "SAPETRO" mai harkar haka da dillan danyen man fetur da makamashin iskar gas.
4. Mohammed Indimi
Mohammed Indimi, dan asalin jihar Borno, shine ya kafa kuma yake jagorantar kamfanin "Oriental Energy Resources, Ltd" mai harkar haka da dillancin danyen man fetur.
Ya kafa kamfanin ne a shekarar 1990 kuma tun bayan lokacin kamfanin yake samun habaka da bunkasar al'amura.
5. Sayyu Dantata
Sayyu ya fara aiki ne a matsayin darektan bangaren Injiniyarin da Sufuri na rukunin kamfanonin Dangote.
Shine ya kafa kuma har yanzu yake jagorantar harkokin kasuwanci na rukunin masana'antun "MRS Holdings Ltd (wanda a baya aka sani da "MRS Group").
Sayyu dan asajin jihar Kano ne kuma yana da dangantaka ta jini da attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng