Yanzu-yanzu: 'Yan kungiyar Boko Haram ta sake kai hari a Borno

Yanzu-yanzu: 'Yan kungiyar Boko Haram ta sake kai hari a Borno

- Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai hari a karamar hukumar Dikwa da ke jihar Borno

- Yan bindigan sun samu shiga cikin garin duk da jami'an tsaro da suka yi musayar wuta da su

- Wani mazaunin garin ya ce jama'a suna ta barin gidajensu suna tserewa domin tsira da ransu

Boko Haram, a ranar Juma'a, sun afka karamar hukumar Dikwa, inda suka rika harbe-harbe bayan fafatawa da jami'an tsaro, a cewar wasu majiyoyi.

Mazauna garin, ciki har da yan gudun hijira sun tarwatse suna neman inda za su tsira sakamakon karar abin fashewa da na harbin bindiga da ya mamaye garin, rahoton jaridar Vanguard.

Yanzu-yanzu: 'Yan kungiyar Boko Haram ta sake kai hari a Borno
Yanzu-yanzu: 'Yan kungiyar Boko Haram ta sake kai hari a Borno. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yan bindiga sun sace limamin Kaduna a hanyarsa na zuwa ɗaurin aure a Niger

A cikin wannan makon, wasu yan ta'addan sun afka karamar hukumar Marte sun tafka ta'adi inda suka kwace iko a garin suka kafa tutarsu a hedkwatar karamar hukumar.

Wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa ya fadi fada wa wakilin Vanguard cikin sakon text cewa, "yan ta'adan sun shiga Dikwa misalin karfe 5.30 na yammacin Juma'a kuma sunyi ta musayar wuta da sojoji har zuwa karfe 9.05 na dare."

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Ƴan Nigeria ba su buƙatar izini kafin su zauna a dazukan Ondo

Bai bayyana ainihin adadin mutanen da suka rasu ba amma yana zargin za a samu wadanda za su mutu daga bangaren yan ta'addan, sojoji da ma farar hula.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel