Mayakan Boko Haram sun kai hari kananan hukumomi 2 a Borno, sun sheke mutane

Mayakan Boko Haram sun kai hari kananan hukumomi 2 a Borno, sun sheke mutane

- Bai kai kwana 2 ba da 'yan Boko Haram suka afka karamar hukumar Biu inda suka lalata daruruwan gidaje yanzu kuma sun kara wani kai harin

- Da daren Talata ne suka afka kananun hukumomin Marte da Gubio dake jihar Borno inda suka budewa wasu mafarauta wuta daga baya sojoji suka fara ragargazarsu

- Sai da 'yan bindigan suka fatattaki sojoji daga mazauninsu kafin su afka sabuwar anguwar Marte suna harbe-harbe jama'a suna gudun neman tsira

Bai wuce kwana 2 ba da 'yan Boko Haram suka afka Egiri, Zira I da II dake karkashin karamar hukumar Biu wanda hakan yayi sanadiyyar asarar gidaje da dama, sun kara kai hari kananun hukumomin Marte da Gubio dake jihar Borno a daren Talata.

Kamar yadda labarai suka gabata, 'yan bindigan sun afka mazaunin 'yan sa kai da mahauta inda suka bude musu wuta har suna kashe wasu suka kuma ji wa wasu raunuka kafin sojoji su mayar musu da harin.

A Marte kuwa sai da 'yan bindigan suka afka anguwar sabuwar Marte da miyagun makamai suna harbe-harbe jama'a na gudun neman tsira.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya gwangwaje 'yan kasuwar Shasha da N18.5m na rage radadi

Mayakan Boko Haram sun kai hari kananan hukumomi 2 a Borno, sun sheke mutane
Mayakan Boko Haram sun kai hari kananan hukumomi 2 a Borno, sun sheke mutane. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Facebook

An samu labarin cewa tun ranar Talata har Laraba da rana sun mamaye garin kafin sojoji su fara mayar musu da hari, Vanguard ta ruwaito.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Marte, Hon. Marte Mohammed Gambomi ya tabbatar da harin da aka kai wa garin Marte.

Ya tabbatar wa da manema labarai cewa an kira shi an sanar dashi yadda 'yan Boko Haram suka afka Marte, amma bai sanar da yawan mutanen da suka kai wa hari ba, sai dai ya ce sun taba gidaje.

A cewarsa; "Eh 'yan Boko Haram sun kai hari Marte a ranar Talata kamar yadda na samu labari, amma jama'a sun tsere."

KU KARANTA: Tsuleliyar budurwa ta rubutawa Don Jazzy wasikar soyayya ranar masoya, ta janyo cece-kuce

A wani labari na daban, tsohon hafsin sojojin kasa na Najeriya, laftanal janar Azubuike Ihejirika mai murabus, ya shiga jam'iyyar APC.

Ya bayyana hakan ne yayin da yayi rijistar jam'iyyar a ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Idan ba a manta ba, ya rike kujerar shugabancin sojin ne daga 2010 zuwa 2014 karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, sannan ya bayyana kudirin komawa jam'iyyar APC din ne a garinsu na Isuikwuato dake mazabar Abia ta arewa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel