Fani-Kayode ya caccaki Saraki a kan ziyarar da ya kaiwa Jonathan
- Femi Fani-Kayode yayi wa Bukola Saraki tatas sakamakon ziyarar da ya kaiwa Jonathan
- Saraki ya kai wa Jonathan ziyara tare da kwamitin sasanci na jam'iyyar PDP a gidansa da ke Abuja
- Amma kuma Fani-Kayode ya ce Saraki bai yi adalci ba da ya hana Jonathan sauya sheka kamar yadda yayi a 2014
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi fani-Kayode ya kalubalanci tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a kan ziyarar da ya kaiwa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Saraki wanda ya shugabanci kwamitin sasanci da tsari na PDP, ya ziyarci Jonathan a gidansa da ke Abuja bayan hasashen cewa Jonathan na shirin komawa jam'iyyar APC.
An fara zargin tsohon shugaban kasa Jonathan zai sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan ganawa da yayi da wasu jiga-jigan jam'iyyar.
KU KARANTA: Sanusi ya bukaci gwamnati ta kayyadewa 'yan Najeriya yawan iyalin da za su haifa
Saraki ya samu rakiyar wasu 'yan kwamitin sasanci na jam'iyyar wadanda suka hada da tsohon sakatren gwamnatin tarayya, Pius Anyim, tsohon gwamna Ibrahim Shema, Liyel Imoke da Ibrahim Dankwabo.
Bayan ziyarar, tsohon shugaban majalisar dattawan ya shawarci masu damun Jonathan a kan ya sauya sheka da su manta da wannan tunanin domin kuwa yana nan daram a PDP, Premium Times ta wallafa.
Amma a wata wallafar da Fani-Kayode yayi a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, ya nuna mamakinsa da yadda Saraki wanda ya juya wa Jonathan baya a 2014 yake shawartarsa da kada ya bar PDP yanzu.
KU KARANTA: Hotunan wakilan FG, IGP da wasu jiga-jigai da suka kai ziyara Niger bayan sace dalibai
A wani labari na daban, wata mummunar gobara ta yi ajalin wani jariri a wani sansanin 'yan gudun hijira dake wuraren titin Mafa a cikin Maiduguri jihar Borno a ranar Talata.
Ganau sun tabbatar da yadda lamarin ya faru da misalin 7:30am na safiya a wani bangare na sansanin amma an samu nasarar kashe gobarar cikin karamin lokaci.
A cewar ganau din: "Wata gobara ta barke da misalin 1pm kuma ta yi sanadiyyar kone tanti da dama dake sansanin."
Wani jariri ya kone kurmus sannan wasu manya biyu sun kone kamar yadda ganau din ya tabbatar.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng