Abdussalami ya ja-kunnen Gwamnoni, ya ce ‘Ku iya bakinku’, ko ku jawo wani yakin basasa

Abdussalami ya ja-kunnen Gwamnoni, ya ce ‘Ku iya bakinku’, ko ku jawo wani yakin basasa

- Janar Abdulsalami Abubakar ya ba Gwamnoni shawara a kan matsalar tsaro

- Abdulsalami Abubakar ya ce Gwamnonin su guji sakin baki su na yin magana

- Tsohon shugaban yake cewa irin haka ya jawo aka yi yakin basasa a 1967-70

Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya ce dole mutanen Najeriya su rungumi zaman lafiya domin a guji abin da ya faru tsakanin shekarar 1967 da 1970.

Da aka yi hira da tsohon shugaban kasar a gidan talabijin na Arise, ya ce idan ba a nemi zaman lafiya ba, Najeriya za ta iya barke wa da wani yakin basasan.

Abdulsalami Abubakar ya ke cewa masu shekaru da yawa, sun san abin da ya auku a lokacin da aka yi yakin Biyafara, kuma ba za su so hakan ya sake faruwa ba.

Ya ce: “Gwamnoni sun samu kansu a wani yanayi mai ban wahala, nauyinsu ne su mulki jihohinsu ba tare da la’akari da su wanene ke zaune a jihohinba.”

KU KARANTA: Hafsohin Sojoji sun sha alwashin magance matsalar rashin tsaro

“Abin takaici ne ace kwatsam rashin jituwa tsakanin kabilu ya na shiga ko ina. Ku na iya ganin yadda ake fatattakar makiyaya a wasu yankuna a jihohin Kudu.”

Tsohon shugaban kasar ya kuma ce: “Sannan ana kashe masu dabbobi. Babu shakka, wannan zai jawo karin zaman dar-dar a kasar nan, kuma har ma ya jawo.”

“Ku na ganin yadda wasu ke kaura daga wani bangaren kasar nan, su na koma wa jihohinsu, inda su ke jin cewa sun fi zama cikin aminci.” Inji Janar Abubakar.

Dattijon ya ce abin da ya ke faru wa ya na maida Najeriya gidan jiya zuwa 1960s, inda a karshe rikicin ya kai ga yin yaki; ‘masu shekaru sun san abin da aka yi.’

Abdussalami ya ja-kunnen Gwamnoni, ya ce ‘Ku iya bakinku’, ko ku jawo wani yakin basasa
Janar Abdulsalami Abubakar Hoto: www.informationng.com
Source: UGC

KU KARANTA: Buhari bai bukatar aikin kwamitin Salami wajen nada shugaban EFCC

“Gwamnoni su kula da irin abin da su ke fada, saboda ana daukar maganganunsu a matsayin umarni, a matsayinsu na gwamnoni su san abin da su ke furta wa.”

Tsohon sojan ya cigaba da ba gwamnonin shawara: “Ka da ku fadi abin da za a yi wa mummunar fassarar cewa ku na yaki da wadanda ba asalin ‘yan jihar ku bane.”

Kwanaki gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya fito ya na kare makiyaya da ke yawo da bindigogi, ya ce ai dole ce ta sa, su ka dauki makamai su na yawo.

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ya bayyana bacin ransa a kan kalaman takwaran na sa. Daga baya gwamnan Ondo ya fito ya na cewa Bala mashirmanci ne.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel