Sababbin Hafsun Sojoji sun bayyana yadda za su bi, su kawo karshen matsalar tsaro

Sababbin Hafsun Sojoji sun bayyana yadda za su bi, su kawo karshen matsalar tsaro

- ‘Yan Majalisar Wakilan Tarayya sun tantance sababbin Hafsoshin Sojojin kasa

- Shugabannin tsaron da aka nada sun yi bayanin yadda za su kawo zaman lafiya

- Hafsohin sun yi alkawarin za su yi kokarin ganin an magance duk matsalar tsaro

Sababbin hafsoshin sojojin Najeriya da ba su dade da shiga ofis ba, sun yi alkawarin inganta harkar tsaro a kasar nan, jaridar Premium Times ta bada wannan rahoto.

Shugabannin tsaron kasar sun bayyana wannan ne a lokacin da su ka bayyana a gaban majalisar tarayya, a garin Abuja, a ranar Laraba, 17 ga watan Fubrairu, 2021.

Hafsoshin sun yi magana a lokuta daban-dabam ne yayin da wani kwamitin tsaro na majalisar wakilan tarayya yake tantance su, domin jin irin shiri da dabarunsu.

Manjo Janar Leo Irabor ya bayyana cewa ya halarci kwas da dama a gida da wajen Najeriya, ya ce zai yi amfani da wannan ilmi da ya samu wajen kawo zaman lafiya.

KU KARANTA: Gwamnati ta zauna da ‘Yan bindiga a kan yaran da aka sace a Neja

Leo Irabor ya ce a matsyinsa na tsohon shugaban dakarun Operation Lafiya Dole’, zai shawo kan matsalar ta’addanci da ake fama da shi musamman a yankin Arewa.

A na shi bangaren, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya sha alwashin jagorantar sojojin kasa ta yadda za su iya yin maganin duk wasu masu tada kafar baya a fadin Najeriya.

Ibrahim Attahiru ya yi alkawarin cewa sojojin kasa za su samu kayan aiki da duk abubuwan da su ke bukata domin ganin sun cin ma burinsu na tsare mutuncin kasar nan.

Auwal Gambo da Isiaka Amao sun bayyana yadda za su yi amfani da matsayinsu domin su taimaka wa takwarorinsu domin ganin matsalar rashin tsaro ta zama tarihi.

KU KARANTA: Tsohon Ministan Buhari ya ce wasu na cin abinci da rashin tsaro

Sababbin Hafsun Sojoji sun bayyana yadda za su bi, su kawo karshen matsalar tsaro
Leo Irabor, Ibrahim Attahiru, Awwal Gambo, da Isiaka Amao Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wadanda ‘yan majalisar su ka tantance su ne: Leo Irabor, Ibrahim Attahiru, Awwal Gambo, da Isiaka Amao.

Ganin an sace yara a makarantar GSS Kagara, Farfesa Taufiq Abdulaziz ya ce za a duba gudun ruwan hafsoshin tsaron da shugaban kasa ya nada da wannan lamari.

Farfesa Abdulaziz ya ce masu garkuwa da mutane su kan hada-kai da Jami’an tsaro wajen yin wannan ta'adi, sannan ya zargi jami'an tsaro da samun kudi daga matsalar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel