Gwamnan jihar Bauchi ya bani kunya, Samuel Ortom na Benue ya caccaki Kaura

Gwamnan jihar Bauchi ya bani kunya, Samuel Ortom na Benue ya caccaki Kaura

- Anan musayar kalamai tsakanin gwamnan jihar Benue da na jihar Bauchi

- Gwamnan Bauchi ya ce dole ne yake sa makiyaya yawo da bindiga don kare kansu

- Gwamnan Ortom ya ce wani doka ya baiwa makiyaya daman rike bindiga

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana bacin ransa kan takwaransa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda ya daura masa laifin halin da Fulani makiyaya ke ciki, rahoton Daily Trust.

Yayin magana a ranar Alhamis, gwamna Bala ya tuhumi Ortom na tsananta rikicin manoma da makyaya ta irin maganganun da yake yi.

Amma mai magana da yawun Ortom, Terver Akase, a martaninsa, ya ce gwamna Ortom ya yi mamakin kalaman gwamna Bala saboda yana kira ga sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya da ya rantse zai kare.

Ya ce yawancin kalaman da Bala Mohammed yayi kawai yana kokarin kare Fulani Makiyaya ne.

Yace: "Gwamna Ortom ya na mamakin shin wani sashen dokokin kasa gwamnan Bauchi ya dogara da shi na goyon bayan Makiyaya masu yawo da manyan makamai."

"Abin takaicin da ke damun gwamna (Ortom) shine wai ya za'ayi mutumin da aka baiwa hakkin kare jama'a ya rika kalaman batar da mutane."

"Ya jaddada cewa akwai bukatan shugabanni su yi hattara wajen yin abubuwan da ka iya kai kasar nan ga halaka."

KU KARANTA: Ana cece-kuce kan shugaban kwamitin Olympics na Qatar don ya ki musafaha da Alkalan wasa mata

Gwamnan jihar Bauchi ya bani kunya, Samuel Ortom na Benue ya caccaki Kaura
Gwamnan jihar Bauchi ya bani kunya, Samuel Ortom na Benue ya caccaki Kaura Credit: Presidency
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kwankwasiyya ta yi Alla-wadai da shirin rusa gadar saman da Ganduje ke kokarin yi

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai tsinanawa yan Nigeria wani abin azo a gani ba a bangaren tsaro.

Ya yi kira ga shugaban kasar ya sake bita dokokin ECOWAS na zirga-zirgan mutane, hada-hadar kayayyaki da ayyuka a yankin Afirka ta Yamma.

Gwamnan ya ce makiyaya daga kasashen ketare suna amfani da damar da dokar ECOWAS din ta basu don shigowa Nigeria su janyo rikici.

Asali: Legit.ng

Online view pixel