Fadar Shugaban kasa Buhari ta tanka Lauyan Ibrahim Magu a kan nadin Shugaban EFCC

Fadar Shugaban kasa Buhari ta tanka Lauyan Ibrahim Magu a kan nadin Shugaban EFCC

- Fadar Shugaban kasa ta yi wa Ibrahim Magu raddi game da nadin Shugaban EFCC

- Wani Lauyan Magu ya soki yadda aka nada wani sabon shugaban Hukumar EFCC

- Garba Shehu yace zaben wanda zai rike EFCC bai da alaka da binciken Ayo Salami

Daya daga cikin hadimin shugaban kasa ya ce mai girma Muhammadu Buhari ya na da ikon ya nada wanda zai jagoranci ragamar hukumar EFCC.

Rahoton binciken da Alkali Ayo Salami su ka yi bai da tasiri ga shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen nada shugaban EFCC inji Garba Shehu.

Jaridar Premium Times ta ce mai ba shugaban Najeriyar shawara a kan harkokin yada labarai da hulda da jama’an ne ya bayyana mata wannan a yau.

Fadar shugaban kasar ta maida martani ne game da wasu surutan da aka ji lauyan Ibrahim Magu watau tsohon shugaban hukumar EFCC, ya fito ya na yi.

KU KARANTA: Gwamnan Legas ya aikawa Aisha Buhari sakon taya murna, Buhari ya yi gum

Wasu sun soki yadda Muhammadu Buhari ya nada wani shugaban EFCC ba tare da an ji sakamakon binciken da kwamitin Ayo Salami su ka yi ba.

Da aka tuntubi Garba Shehu a kan batun, sai ya ce rahoton binciken Ibrahim Magu bai da alaka da ikon da shugaban kasa yake da shi na nada shugaban EFCC.

Hadimin ya ce: “Ikon nada shugaban EFCC bai ta’allaka da rahoton binciken ko wani rahoto na dabam ba. A wajen aiki da doka, babu abin da ya hada su.”

“Rahoton kwamitin binciken wani abu ne na dabam kuma gaba daya.” Inji Malam Garba Shehu.

KU KARANTA: Da mu na yara tsayawa mu ke ayi a gwabza da 'Yan bindiga - Ministan tsaro

Fadar Shugaban kasa Buhari ta tanka Lauyan Ibrahim Magu a kan nadin Shugaban EFCC
Malam Garba Shehu Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

“Kundin tsarin mulki ya yi bayani karara, ya ba shugaban kasa ikon nada wadanda za su rike wannan kujera, kuma ya ba shi ikon tsige wadannan mutane.”

Kwanan nan wani Lauyan Ibrahim Magu ya koka game da yadda aka fatattake shi, aka sa kwamiti ya yi bincike shi abin da ya gudanar a lokacin ya na EFCC.

Tosin Ojaomo ya so ace an fito an yi bayanin abin da aka gano a binciken da Ayo Salami su ka yi.

A karshe sai dai aka ji cewa an nada Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban EFCC, don haka ya ce ba ayi wa Magu da sauran Jami’an da aka bincika adalci ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel