Hotunan wakilan FG, IGP da wasu jiga-jigai da suka kai ziyara Niger bayan sace dalibai

Hotunan wakilan FG, IGP da wasu jiga-jigai da suka kai ziyara Niger bayan sace dalibai

- Wakilan gwamnatin tarayya da suka hada da ministoci tare da NSA sun isa jihar Neja

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura wakilai domin tsara yadda za a ceto dalibai

- A safiyar yau Laraba ne aka sace dalibai da malamai na kwalejin kimiyya da ke Kagara

Wasu wakilan gwamnatin tarayya da suka hada da mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa, Mohammed Babagana Munguno da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu a halin yanzu suna babban birnin jihar neja.

Daga cikin wakilan akwai ministan yada labarai da al'adu, lai Mohammed, Ministan cikin gida, Rauf Argebesola da ministan al'amuran 'yan sanda, Muhammed Maigari Dingyadi.

Wakilan suna jihar Neja ne a kokarinsu na ceto daliban makarantar sakandare da aka yi garkuwa da su a kwalejin kimiyya da ke Kagara ta jihar Neja.

KU KARANTA: Gwamnonin arewa maso yamma sun gana da mai bada shawara kan tsaron kasa

Hotunan wakilan FG, IGP da wasu jiga-jigai da suka kai ziyara Niger bayan sace dalibai
Hotunan wakilan FG, IGP da wasu jiga-jigai da suka kai ziyara Niger bayan sace dalibai. Hoto daga @ChannelsTV
Source: Twitter

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura su Minna da ke jihar Neja. Sun hada da kungiyar shugabannin tsaro da za su hada yadda za a tseratar da yaran.

Wasu 'yan bindiga a ranar Laraba da safe sun shiga makarantar kwanan wurin karfe 2:00am sanye da kayan sojoji inda suka dinga harbe-harbe a iska.

Hotunan wakilan FG, IGP da wasu jiga-jigai da suka kai ziyara Niger bayan sace dalibai
Hotunan wakilan FG, IGP da wasu jiga-jigai da suka kai ziyara Niger bayan sace dalibai. Hoto daga @ChannelsTV
Source: Twitter

Shugaban makarantar wanda ya sha da kyar sakamakon harin ya tabbatarwa da gidan talabijin na Channels cewa 'yan bindigan sun fara ne daga kwatas din malamai inda suka kwashe wasu.

Wasu majiyoyi sun ce wasu daga cikin daliban sun tsere bayan samamen amma ana cigaba da kirga su domin tabbatar da yawan daliban da ake sace.

Hotunan wakilan FG, IGP da wasu jiga-jigai da suka kai ziyara Niger bayan sace dalibai
Hotunan wakilan FG, IGP da wasu jiga-jigai da suka kai ziyara Niger bayan sace dalibai.Hoto daga @ChannelsTV
Source: Twitter

KU KARANTA: Tsuleliyar budurwa ta rubutawa Don Jazzy wasikar soyayya ranar masoya, ta janyo cece-kuce

A wani labari na daban, yara kanana bakwai sun samu rauni sakamakon hatsarin da ya auku bayan fashewar wani abu a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, jaridar The Cable ta ruwaito.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar a ranar Talata.

Kamar yadda rahotannin tsaro suka tabbatar, yaran da ke wasa a yankin sun dauka abu daga wata gona makusanciya. Ya ce abun ya fashe yayin da yaran ke wasa da shi.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel