Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutane a sabon harin da suka kai Neja

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutane a sabon harin da suka kai Neja

- Yan bindiga sun sake afkawa wasu kauyuka a karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger inda suka halaka mutane

- Kauyukan da aka kai wa harin sun hada da Sarkin Zama, Bakin Kogi (Lagbe), Siyiko da wasu kauyukan da ke makwabtaka da su

- Yan bindigan sun kai wannan hare-haren ne bayan harin da aka kai makarantar sakandare ta garin Kagara inda aka sace dalibai da ma'aikata

Yan bindiga sun sake kai hari a wasu garuruwa a mazabar Gurmana da ke karamar hukumar Shiroro na jihar Niger, Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa an kai hari a kauyukan Sarkin Zama, Bakin Kogi (Lagbe), Siyiko da wasu kauyukan da ke kusa da su inda yan bindigan suka shafe awanni suna cin karensu babu babbaka.

DUBA WANNAN: Haramta wa'azi: Abduljabbar ya roƙi lauyoyi su janye ƙarar da suka shigar kan Ganduje

Yanzu yanzu: Rayyuka sun salwanta sakamakon sabon harin da yan bindiga suka kai a Neja
Yanzu yanzu: Rayyuka sun salwanta sakamakon sabon harin da yan bindiga suka kai a Neja. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

A cewar daya daga cikin shugabannin kungiyar matasa masu kishin Shiroro, Sani Yusuf Kokki, an kashe wasu mazauna garuruwan yayin harin da ya faru awanni bayan sace dalibai da ma'aikata a kwallejin kimiyya ta Kagara da ke karamar hukumar Rafi.

KU KARANTA: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'

"Ana kawo hare hare da dama hakan yasa mutanen garuruwan ke rayuwa cikin fargaba da tsoron miyagun yan bindigan. An kyalle mutane masu son zaman lafiya da ba za su iya kare kansu ba," Kokki ya ce a cikin jawabinsa.

Bayan harin na Kagara, Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin tsaro su tabbatar sun ceto wadanda aka yi garkuwar da su.

A cikin sanarwar da kakakinsa Mallam Garba Shehu ya fitar a madadinsa, shugaban kasar ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin kiyayye yan Nigeria.

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.

Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel