Yara 7 sun samu rauni bayan 'abu mai fashewa' ya tarwatse suna wasa dashi a Kaduna

Yara 7 sun samu rauni bayan 'abu mai fashewa' ya tarwatse suna wasa dashi a Kaduna

- Wani abu mai fashewa ya tashi da wasu yara kanana 7 a karamar hukumar Igabi ta Kaduna

- Kamar yadda kwamishinan tsaron cikin gida ya sanar, lamarin ya faru ne a ranar Talata

- Yaran sun tsinto abun ne daga gona inda suka dinga wasa da shi har ya fashe

Yara kanana bakwai sun samu rauni sakamakon hatsarin da ya auku bayan fashewar wani abu a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, jaridar The Cable ta ruwaito.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar a ranar Talata.

Kamar yadda rahotannin tsaro suka tabbatar, yaran da ke wasa a yankin sun dauka abu daga wata gona makusanciya.

Ya ce abun ya fashe yayin da yaran ke wasa da shi.

KU KARANTA: Tsuleliyar budurwa ta rubutawa Don Jazzy wasikar soyayya ranar masoya, ta janyo cece-kuce

Tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel ya koma jam'iyyar APC
Tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel ya koma jam'iyyar APC. Hoto daga @Thecableng
Source: UGC

"Rahotannin daga jami'an tsaro sun tabbatar da cewa wani abu mai fashewa ya tashi a Ungwan Mangwaro da ke karamar hukumar Igabi," takardar tace.

"Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, yaran suna wasa a yankin sun samo abun daga wata gona inda suka fara wasa da shi ba tare da sun san mene ne ba.

"A hakan ne suka tashe shi sakamakon taba shi da suka dinga yi.

"Yara bakwai ne suka raunata kuma yanzu haka suna samun kulawar likitoci a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Shika."

Aruwan ya ce gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce da sauki tunda ba a rasa rai ba.

Gwamnan ya yi kira ga jami'an tsaro da su tabbatar da sun gano abinda ya kawo aukuwar lamarin.

Aruwan ya kara da shawartar jama'a da su kai rahoto ga jami'an tsaro na duk abinda suka samu wanda basu gane ba.

KU KARANTA: Lai Mohammed ya bukaci a soke sabunta rijistar 'yan APC ta jihar Kwara

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Bauchi ta kara haske a kan jawabin Gwamna Bala Mohammed inda yace makiyaya su dinga yawo da AK-47 domin baiwa kansu kariya.

A wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi 14 ga watan Fabrairu, Mukhtar Gidado wanda babban mai baiwa gwamnan shawara ne a kafafen sada zumunta ya ce ba a fahimci tsokacin ubangidansa bane, The Punch ta wallafa.

Idan za a tuna, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bukaci makiyaya su dinga yawo da AK-47 domin shawo kan matsalar satar shanunsu da ake yi.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel