Hukuma ta yi wuf, ta yi magana bayan an fara tono zargin badakala a kan sabon Shugaban EFCC

Hukuma ta yi wuf, ta yi magana bayan an fara tono zargin badakala a kan sabon Shugaban EFCC

- Hukumar EFCC ta fito ta wanke Abdulrasheed Bawa daga zargin masu zargi

- Ana jifan Bawa da laifin karkatar da wasu motocin da EFCC ta karbe a 2019

- Wilson Uwujaren ya ce sam babu hannun sabon shugaban EFCC a badakalar

A ranar Talata, 16 ga watan Fubrairu, hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin Najeriya zagon-kasa, ta yi magana a kan zargin da ke kan Abdulrasheed Bawa.

Jim kadan bayan shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban EFCC, wasu rahotanni su ka fara yawo game da shi a jaridu.

Punch ta bayyana cewa hukumar EFCC ta yi maza, ta fito ta wanke sabon shugaban na ta, ta ce sam babu wani laifi da ake zarginsa da shi, kamar yadda wasu ke fada.

Mai magana da yawun bakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya musanya wannan zargi a wani jawabi da ya fitar a ranar Talata, inda ya wanke Abdulrasheed Bawa.

KU KARANTA: Buhari ya nada sabon Shugaban EFCC

Uwujaren ya ce maganar cewa an sauke Bawa daga kujerar shugaban babban ofishin EFCC na Fatakwal saboda saida wasu manyan motoci da aka kama ba gaskiya ba ne.

Ga abin da jawabin ya ce:

“A matsayinasa na shugaban ofishin Fatakwal a 2019, nauyin da ke kan Bawa ba su hada da saida kadarorin da hukumar ta karbe ba, akwai wani sashen da ke kula da wannan.”

“Domin cire shakku, an yi gwanjon motocin da aka karbe a Fatakwal ne bayan Bawa ya bar ofis. Don haka babu hikima a zarge shi da hannu a abin da ba shi ya gudanar ba."

Hukuma ta yi wuf, ta yi magana bayan an fara tono zargin badakala a kan sabon Shugaban EFCC
Sabon Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Daurin gindi: 'Yan Sanda wallafa sunayen Fulani da ake kara a kotu - Buhari

Jawabin ya ce: “Gwanjon motoci da aka yi a ofishin Fatakwal ya na cikin binciken da kwamitin Ayo Salami ya yi, wanda har ya jawo aka dakatar da wasu jami’ai daga aiki.”

“Hukumar ta na kira ga jama’a su yi watsi da rahotannin karyar da ke yawo, wanda mu ka yi imani wasu miyagu ne su ka kitsa su domin bata sunan sabon shugaban EFCC.”

A jiya ne ku ku ji cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Matashin Jami’i mai shekara 40 ya jagoranci aikin Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya.

Wannan jami’in ya na cikin sahun farko da Nudu Ribadu ya dauka aiki bayan an kafa EFCC.

Mista Abdulrasheed Bawa, mutumin Jega, jihar Kebbi ne, ya yi Digirinsa a fannin tattalin arziki, da digirgir a ilmin harkokin kasar waje a Jami'ar Usman Danfodio, Jihar Sokoto.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel