Da duminsa: COAS na Goodluck Jonathan ya sauya sheka, ya koma jam'iyyar APC

Da duminsa: COAS na Goodluck Jonathan ya sauya sheka, ya koma jam'iyyar APC

- Tsohon hafsin sojojin kasa, laftanal janar Azubuike Ihejirika mai ritaya, ya koma jam'iyyar APC

- Ya bayyana batun canja shekarsa ne tare da yin rijistar zama cikakken dan jam'iyyar a ranar Talata

- Amma janar Ihejirika ya rike kujerar shugabancin sojin kasa ne lokacin mulkin Goodluck Jonathan

Tsohon hafsin sojojin kasa na Najeriya, laftanal janar Azubuike Ihejirika mai murabus, ya shiga jam'iyyar APC.

Ya bayyana hakan ne yayin da yayi rijistar jam'iyyar a ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Idan ba a manta ba, ya rike kujerar shugabancin sojin ne daga 2010 zuwa 2014 karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, sannan ya bayyana kudirin komawa jam'iyyar APC din ne a garinsu na Isuikwuato dake mazabar Abia ta arewa.

KU KARANTA: Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya rasa shugaban ma'aikatansa

Da duminsa: COAS na Goodluck Jonathan ya sauya sheka, ya koma jam'iyyar APC
Da duminsa: COAS na Goodluck Jonathan ya sauya sheka, ya koma jam'iyyar APC. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

Tsohon COAS din ya yi rijistar zama cikakken dan jam'iyyar ne a gundumar Ezere 2.

Shugaban jam'iyyar na gundumar, Iheanyi Chukwu a gaban jiga-jigan jam'iyyar, cikinsu har da sakataren jam'iyyar na jihar, Kalu; Shugabar matan jam'iyyar Perfect Okorie; Lady Franca Osuwa; shugaba masu rijista na APC a jihar Abia, Ambasada Bala Mohammed Mairiga; Chief Mohammed Ogah; Dr Lilian Obenwa; shugabar jam'iyyar ta Abia ta arewa; Chief Chris Ajah da sauransu.

Idan ba a manta ba a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, shugaban jam'iyyar APC a jihar Abia, Kalu, ya roki Ihejirika ya shiga jam'iyyar.

"Komawar janar Ihejirika jam'iyyar APC babbar nasara ce kuma wajibi ne mu yaba masa bisa dagewarsa wurin daukar irin wannan babban matakin.

"Muna masu tabbatar masa da cewa jam'iyyarmu za ta samar masa da cigaba," cewar Kalu.

KU KARANTA: Saboda kariya nace makiyaya su dinga yawo da AK47, Gwamnan Bauchi ya kare kansa

Tsohon COAS din ya bayyana dalilan da suka sanya ya shiga jam'iyyar APC, inda yace ya shiga jam'iyyar ne don ya bayar da gudunmawarsa ga demokradiyya.

A cewarsa, "Na kwashe tsawon shekaru 38 ina yi wa kasata hidima a matsayina na soja, kuma na fahimci abubuwa da dama. Don haka zama na wajen gwamnati asara ne."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel