Faransa ga Afirka ta Yamma: Ku kara kaimi wajen yaki da 'yan ta'adda

Faransa ga Afirka ta Yamma: Ku kara kaimi wajen yaki da 'yan ta'adda

- Shugaban kasar Faransa ya gargadi shugabannin Afrika da su kara kaimi a yakar 'yan ta'adda

- Ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Afrika su mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro

- Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta tallafa, amma ba zai yiwu yayi hakan nan take ba

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci shugabannin kasashen Afirka ta Yamma da su kara kaimi a yakin da ake yi da masu tada kayar baya a yankin Sahel ta fuskokin soja da siyasa, tare da goyon baya daga kasashen duniya.

Macron ya shiga taron ne ta hanyar bidiyo da ake gudanarwa a NDjamena, Chadi, tare da shugabannin kasashen Mali, Burkina Faso, Chadi, Niger da Mauritania, The Natiaon ta ruwaito.

"Kalubalen taron na NDjamena shi ne daukar mataki na gaba, da kara karfi," in ji Macron daga Paris.

KU KARANTA: Idan Fani Kayode ya koma APC, to PDP ce zata ruguje ba shi ba, in ji jigon PDP

Faransa ga Afirka ta Yamma: Ku kara kaimi wajen yaki da masu 'yan ta'adda
Faransa ga Afirka ta Yamma: Ku kara kaimi wajen yaki da masu 'yan ta'adda Hoto: US News & World Report
Source: UGC

"Bai kamata mu sake da matsin lamba kan kungiyoyin 'yan ta'adda ba."

Ya ce ya kamata ayyukan soji su ci gaba da mai da hankali kan yankin da ke kan iyaka da Mali, Nijar da Burkina Faso, cibiyar yaki da kungiyoyin 'yan bindiga.

Macron ya kuma ce Faransa ba ta da wani shiri nan take na daidaita dakarunta a yankin Sahel na Afirka, kuma duk wani sauye-sauye zai dogara ne da sauran kasashen da ke ba da gudummawar sojoji, a wani taron manema labarai a ranar Talata bayan taron.

Macron ya ce "Babu shakka za a samar da muhimman sauye-sauye ga tsarin sojanmu a yankin Sahel a kan kari, amma ba za su faru nan take ba," in ji Macron.

Faransa, tsohuwar yankin da ke karkashin mulkin mallaka, na neman dabarun ficewa bayan kwashe tsahon shekaru na tsoma bakin sojoji kan kungiyoyin mayaka.

Aikinta na yaki da ta'addanci a cikin Sahel ya ci biliyoyin kudi kuma ya ga sojojin Faransa 55 da aka kashe, amma har yanzu ana ci gaba da rikici tare da alamun yana yaduwa zuwa Yammacin Afirka na bakin teku.

KU KARANTA: Bayan jihar Oyo, gwamnonin Arewa sun garzaya jihar Ogun

A wani labarin, Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da gwamnoni hudu daga yankin arewacin Najeriya a yanzu haka suna ganawa a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Taron ya kunshi manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabanin Fulani, manoma da sarakunan gargajiya a jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel