Invictus Obi: Mutumin Najeriya da ya yi damfarar Naira Biliyan 5 zai shafe shekaru 10 a kurkuku

Invictus Obi: Mutumin Najeriya da ya yi damfarar Naira Biliyan 5 zai shafe shekaru 10 a kurkuku

- Kotun Amurka ta yanke hukuncin daurin shekara 10 a kan Obinwanne Okeke

- Rebecca Beach Smith ce ta samu Obinwanne Okeke da laifin damfarar jama’a

- FBI ta ce matashin ya damfari Bayin Allah abin da ya kai akalla Dala miliyan 11

A ranar Talatar nan ne wata kotun Amurka ta yanke wa Obinwanne Okeke daurin shekaru 10 a gidan yari bayan an kama shi da laifin damfarar jama’a.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto cewa an daure Obinwanne Okeke wanda aka fi sani da Invictus Obi sakamakon satar kimanin Dala miliyan 11.

Wannan mutumi wanda ya fito daga Najeriya, ya yi amfani da fasahar na’ura mai kwakwalwa, ya rika damfarar Bayin Allah ta hanyar shafukan yanar gizo.

Wani babban jami’in shari’a na garin Virgnia, kasar Amurka, Raj Parekh ya jero laifuffukan Okeke.

KU KARANTA: Invictus Obi ya saci $11m a kasar Amurka

Raj Parekh ya ji dadin hukuncin da kotu ta yanke a kan wannan ‘dan damfara wanda ya yi ta’adi tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, a karshe ya shiga hannu.

Mista Raj Parekh ya ce hukuncin da Alkali Rebecca Beach Smith ta dauka, ya nuna lallai hukumar FBI da gaske ta ke yi wajen gano ‘yan damfara da zamba.

FBI ta ce Invictus Obi ya kware wajen zamba da damfara da fake wa da sunan wasu, inda ya kan aika sakon karya ta akwatin e-mail, daga nan ya bi, ya sace masu kudi.

Wannan ja’irin matashi ya damfari kamfanin Unatrac Holding Limited wadanda su ke saida manyan motoci a kasar waje, ya samu bayanan sirrinsu ta yanar gizo.

KU KARANTA: Lauyoyin EFCC sun bankado yadda Oduah ta sace kudin Gwamnati

Invictus Obi: Mutumin Najeriya da ya yi damfarar Naira Biliyan 5 zai shafe shekaru 10 a kurkuku
Mr. Obinwanne Okeke
Source: UGC

Takardun kotu sun nuna cewa Okeke mai shekara 33 ya bude wani kamfaninsa da ake kira Invictus Group a Najeriya, wanda ya ke da rassa har a wasu kasashen.

Tun a baya kun ji cewa gawurtaccen Ɗan Yahoo-Yahoo din zai iya shafe shekaru 20 a kurkukun Amurka, idan aka tabbatar cewa Okeke ya aikata laifin da ake zarginsa.

Invictus Obi ya amsa laifinsa a gaban Alkali a kotu lokacin da aka fara shari'a da shi a Virginia.

Obinwanne Okeke da abokan mugun aikinsa sun bayyana ne a gaban Alkali mai shari’a. A wancan lokaci Robert Krask ne wanda ya saurari karar da FBI ta shigar.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel