Laifin damfara: Invictus Obi ya saci $11m a kasar Amurka

Laifin damfara: Invictus Obi ya saci $11m a kasar Amurka

Jaridar Punch ta rahoto cewa a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni, 2020, Ɗan kasuwan Najeriya, Obinwanne Okeke wanda aka fi sani da Invictus Obi ya amsa laifinsa a gaban Alkali a kotu.

Invictus Obi ya shaidawa kuliya cewa ya aikata laifin da ake zarginsa da shi. An gabatar da Mista Obinwanne Okeke ne a gaban wani babban kotu da ke shiyyar Virginia a kasar Amurka.

Obinwanne Okeke da abokan mugun aikinsa sun bayyana ne a gaban Alkali mai shari’a Robert Krask wanda ya saurari karar da ake yi a kansu na laifin sata, damfara da wasu laifuffuka.

Gwamnatin Amurka ta ce Okeke mai shekara 32 ya na da wani kamfani mai suna Invictus Group wanda aka rika amfani da shi tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019 wajen karkatar da kudin sata.

Ma’aikatar shari’a ta kasar Amurka ta ce Obinwanne Okeke ya saci Dala miliyan 11 daga hannun wani kamfani. Idan aka yi lissafin wannan makudan kudi, sun haura Naira biliyan 4.262.

Da aka kirawa Obinwanne Okeke laifuffukansa, ya amsa cewa ya aikatasu.

KU KARANTA: EFCC ta yi nasarar daure wanda ya damfari Zaurawa a jihar Borno

Laifin damfara: Invictus Obi ya saci $11m a kasar Amurka
Takardun shari'ar Invictus Obi Hoto: The Cable
Asali: UGC

“Wadanda ake zargin su na samun bayanan daruruwan mutanen da su ke damfara a yankin gabashin Virginia da sauran wurare.” Inji ma’aikatar shari’ar gwamnatin kasar.

“Daga cikin badakalar, Okeke da wasu su kan aika sakon email na bogi su na harin Unatrac Holding Limited, kamfanin da ke fitar da kayan motocin noma da kayan gona.”

“A Afrilun 2019, shugaban kamfanin Unatrac ya fadawa tarkon sakon Okeke wanda ya ba su damar satar bayanansa, su ka yi masa kutse. Miyagun sun tura bukatun kudi, inda su ka aika takardun ciniki na bogi.”

Ma'aikatar ta ce: “Okeke ya na da hannu a yunkurin damfarar kamfanin Unatrac, ya saci kudi har fam Dala miliyan 11, ya aika zuwa kasashen ketare.”

Jawabin ya kara da cewa: “Okeke ya amsa cewa ya aikata laifin damfara.”

Za a iya daure Okeke na tsawon shekara 20 a gidan yari idan aka kammala wannan shari’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng